logo

HAUSA

Mata da yara sun fi fuskantar fadawa tarkon masu safarar mutane ta hanyar Intanet

2022-09-05 20:26:06 CRI

A halin yanzu a duk duniya, laifin fataucin mutane ya mamaye yanar gizo, yayin da ake samun yaduwar cutar COVID-19, da karuwar sha'awar mutane ta sayen kayan yau da kullum a kan yanar gizo. A cewar shafin yanar gizo na MDD, Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres ya bayyana cewa, munanan laifuka na safarar bil'adama, babban cin zarafi ne da take hakki, da tsaro da mutunci na bil'adama. Abin bakin ciki shi ne, matsalar tana kara ta'azzara, kuma akasarin mutanen da ake fataucinsu da aka gano a duniya mata ne da yara mata.

Kwararru da dama sun bayar da sanarwa a ranar 30 ga watan Yuli, wato ranar yaki da fataucin mutane ta duniya, inda suka nuna matukar damuwarsu game da hadarin da ke tattare da fataucin mutanen da suka rasa gidajensu sakamakon rikici, ciki har da yara.

Sanarwar ta ce, yanayin rikice-rikice na kara samar da damammaki ga fataucin bil adama. 'Yan gudun hijira, mutanen da suka rasa matsugunansu da marasa galihu sun fi fuskantar cin zarafi.

Haka zalika, fataucin mutane masu shekarun haihuwa daban-daban, wata dabara ce da kungiyoyi masu dauke da makamai ke amfani da su, wanda kuma ke haifar da tashe-tashen hankula, da rikice-rikice, da kawo cikas ga shirin samar da zaman lafiya.

Masana sun nuna cewa, irin hadurran dake abkuwa a lokutan rikici, suna da alaka da rashin daidaiton tsarin da ake da su, da nuna wariya dangane da jinsi da launin fata, talauci, da rashin ci gaban tsarin kare yara.

A lokaci guda kuma, a yayin rikice-rikice, ana yin fataucin mutane ba tare da an hukunta su ba, kana ba a daukar iasassun matakai don tinkarar matsalar, ciki har da sa ido, ba da rahoto ko bincike.

Masanan sun ce, “Majalisar ta kara fahimtar alakar da ke tsakanin ayyukan kungiyoyin masu dauke da makamai da safarar yara, da safarar mutane, dangane da cin zarafin mata a yayin rikice-rikice. Amma, duk da wannan amincewa da aka yi, har yanzu ba’a iya dora laifi kan wadanda suka aikata laiffukan yadda ya kamata ba, kuma matakan kariya da aka dauka ba su da inganci."

Bugu da kari kuma, yaran da aka yi fataucin su a cikin yanayin na rikici, da kyar suke iya samun taimako, kariya da kulawa da suka cancanta ba.

Masanan sun jaddada bukatar a shigar da matakan hana fataucin bil-Adama, a cikin ayyukan dukkan masu aikin jin kai da kariya, da kuma ajandar mata, zaman lafiya da tsaro, da kuma matakan samar da zaman lafiya da tabbatar da zaman lafiya. A sa'i daya kuma, ana bukatar daukar matakan gaggawa, don magance matsalolin rashin gidajen kwana da rikice-rikice sakamakon sauyin yanayi, don tabbatar da an yi kandagarkin fataucin mutane yadda ya kamata.

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa, ba a gudanar da ayyukan kariya yadda yakamata ga 'yan gudun hijira, bakin haure da wadanda aka yi fataucinsu, a kan yi balaguron su daga yankin Sahel, da yankin kahon Afirka zuwa arewacin Afirka da Turai.

Sabon rahoton da aka kaddamar game da fataucin mutane, ya shafi kasashe 12, da suka hada da Burkina Faso, Kamaru, Chadi, Cote d'Ivoire, Djibouti, Habasha, Mali, Mauritania, Morocco, Niger, Somalia da kuma Sudan.

Rahoton sun nuna cewa, wasu mutane an yi watsi da su sun mutu a cikin jeji, yayin da wasu suka sha fama da cin zarafi ta hanyar jima'i, da yin garkuwa da su don neman fansa, da azabtarwa, da kuma cin zarafi iri daban daban ta fuskokin jiki da tunani.

Vincent Cochetel, Wakilin musamman na Majalisar Dinkin Duniya dake kula da yankin yamma da tsakiyar Bahar Rum, ya nuna cewa, kasashe daban daban, da hukumomin Majalisar Dinkin Duniya, da kungiyoyin fararen hula, da kungiyoyi masu zaman kansu, suna bukatar su rubanya kokarinsu na aiwatar da tsare-tsaren kasa da kasa, ciki har da irin su yarjejeniyar Palermo ta Majalisar Dinkin Duniya, kan fataucin bil adama da safarar mutane, da mayar da hakan a matsayin mafi kyawun hanyoyin hada kai don ceton rayuka da yaki da wadannan laifuka.

A watan Afrilun bana wato shekarar 2022, Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD (UNHCR), ta fitar da wata sabuwar dabara, don karewa, da ceton rayuka a tafiye-tafiyensu masu hadari, kana da samar da mafita ga wadannan 'yan gudun hijira, yayin da suke kan hanyoyin ratsa tsakiyar da yammacin Bahar Rum, da Tekun Atlantika zuwa Turai. Dabarar ta kunshi yin kira da a samar da dala miliyan 163.5, don taimakawa, da kuma kare dubban 'yan gudun hijira da sauran su. Amma kashi 30% na kudaden ne aka samu a halin yanzu.

Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres ya nuna cewa, yaduwar annobar COVID-19 ta raba yara da abokansu da juna, don haka a yawancin lokuta, suna kasancewa su kadai ko kuma shiga yanar gizo.

Masu fataucin bil’adama suna yin alkawuran karya a kan dandamalin yanar gizo, don yaudara da daukar wadanda abin ya shafa. Ban da wannan kuma, suna yada munanan abubuwan da suka tsara a yanar gizo mai hadari, ciki har da wasu abubuwan da suka yi ta hanyar lalata da yara.

Hanyoyin fasaha na yanar gizo kuma, suna ba wa wasu mutane damar boye asalinsu, a yayin da suke neman masu kallon yanar gizo su samar da wasu bayanai masu hadari, ta yadda hakan ke ba da gudummawa ga ayyukan fataucin mutane.

Antonio Guterres ya ce, “Fasaha na iya saukake fataucin mutane, haka nan za ta iya zama babban kayan aiki na yakar wannan mugun aiki. Wannan shi ne ainihin abin da ake fatan bayyanawa, a matsayin taken ranar yaki da fataucin bil’adama ta duniya ta bana, wato 'Amfani da Fasaha, da Kandagarkin Amfani da Ita ta hanyar da ba ta Dace ba'.

Haka zalika, sakatare-Janar ya ba da shawarar kaddamar da wata yarjejeniyar fasahar zamani ta duniya, wadda ke da nufin cimma matsaya a duniya cewa, yana da muhimmanci a gudanar da harkoki yadda ya kamata a yanar gizo.