logo

HAUSA

Masu sa ido kan tsaron Sudan ta Kudu sun amince da tsawaita wa’adin gwamnatin riko

2022-09-02 13:08:24 CMG Hausa

Daukacin masu sa ido kan yanayin tsaro a kasar Sudan ta Kudu, sun kada kuri’ar amincewa da tsawaita wa’adin gwamnatin riko na kasar da shekaru 2.

Charles Tai Gituai, shugaban hukumar sa ido da nazarin yanayin zaman lafiya da aka farfado da ita wato (R-JMEC), ya ce 2 cikin 3 na masu kada kuri’a a hukumar, sun amince da tsawaita wa’adin bisa tanadin da aka yi cikin yarjejeniyar warware rikicin kasar da aka farfado da ita.

Daga cikin mambobin da ba su kada kuri’a ba, akwai Amurka da Norway da Birtaniya, wadanda suka bukaci a ware watanni 3 domin tuntubar bangarorin masu ruwa da tsaki a yarjejeniyar, kafin tsawaita wa’adin.

Charles Gituai ya bayyana cewa, bisa tsarin yi wa kundin tsarin mulki garambawul da aka gabatar cikin kundin tsarin mulkin gwamnatin rikon, tsawaita wa’adin da watanni 24 na bukatar sa hannun majalisar dokokin kasar ta riko.

Ya kuma bukaci dukkan bangarorin dake cikin yarjejeniyar, su hau teburin tattaunawa, kuma su hada hannu wajen inganta sake gina aminci da kwarin gwiwa kan tsarin wanzar da zaman lafiya, ta hanyar daukar matakai masu karfi na magance dukkan muhimman abubuwan dake kawo tsaiko ga aiwatar da yarjejeniyar ta zaman lafiya.  (Fa’iza Mustapha)