logo

HAUSA

Liu Yuxi ya zama sabon wakilin musamman na gwamnatin kasar Sin mai kula da harkokin Afirka

2022-09-01 16:40:26 CMG Hausa

A yayin taron ’yan jarida na yau da kullum da ma’aikatar harkokin wajen Sin ta gudanar jiya Laraba, kakakin ma’aikatar Zhao Lijian ya sanar da cewa, gwamnatin Sin ta nada Liu Yuxi a matsayin sabon wakilin musamman na gwamnatin kasar Sin mai kula da harkokin Afirka don maye gurbin jakada madam Xu Jinghu.

Zhao ya nuna cewa, yayin da jakada Xu Jinghu take rike da wannan mukami, ta himmatu wajen sada zumunta da hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka a fannoni daban daban. Sannan ta yi kokarin yin mu’ammala da bangarorin kasa da kasa game da harkokin Afirka. Har ma ta ba da muhimmiyar gudummawa wajen inganta dangantakar Sin da kasashen Afirka, da sanya bangarori daban daban da su kara fahimta da sanin hadin gwiwar da ake yi tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka.

Zhao Lijian ya kara da cewa, jakada Liu Yuxi, wani babban jami’in diplomassiya na kasar Sin, kuma shi ne tsohon jakadan Sin a Togo, kuma shugaban tawagar wakilan kasar Sin a hedkwatar kungiyar tarayyar Afirka, ya fahimci al’amuran da suka shafi Afirka kwarai da gaske.

Jakada Liu yana fatan kulla alakar aiki mai karfi tare da bangarori daban daban, ci gaba da karfafa mu’ammala da hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kungiyoyin kasashen Afirka da na nahiyar. Ya tabbatar da cewa, zai yi aikin ka’in da na’in wajen tabbatar da ganin kasashen Afirka sun samu ci gaba cikin lumana, da kuma ci gaba da sada zmunta tsakanin Sin da Afirka. (Safiyah Ma)