logo

HAUSA

Bikin baje kolin cinikayyar hidimomi na kasa da kasa ya shaida fatan kasar Sin na cimma moriyar bai daya

2022-09-01 19:13:07 CMG Hausa

Yayin da ake ci gaba da gudanar da bikin baje kolin cinikayyar hidimomi na kasa da kasa na shekarar 2022 ko CIFTIS a takaice, a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, masharhanta na ci gaba da bayyana fa’idojin wannan baje koli, da ma yadda yake kara haskaka manufar kasar Sin, ta ingiza cudanyar sassan kasa da kasa, da samar da ci gaba na bai daya ga dukkanin bil adama.

Fannin cinikayyar hidimomi na nufin saye ko sayar da hidimomi, wadanda ba su shafi kayan da ake sarrafawa ba, wato biyan kudi domin samun hidimomi kamar na sufuri, yawon bude ido, harkokin sadarwa, tallace-tallace, lissafi da aikin akanta, da musayar bayanai da dai sauran su.

A bana, baje kolin cinikayyar hidimomi na kasa da kasa na CIFTIS, wanda birnin Beijing ke karbar bakunci, ya hallara manyan baki 189 daga ciki da wajen kasar, baya ga kasashe da hukumomin kasa da kasa kimanin 71 da suke halartarsa. Babban burin kasar Sin na samar da wannan dandali dai shi ne kara bude kofa ga waje, da zurfafa hadin gwiwa domin ingiza kirkire-kirkire, wanda hakan wata muhimmiyar gudummawa ce ga ci gaban fannin ba da hidima na duniya baki daya.

A halin da ake ciki, wannan fanni na cinikayyar ba da hidima na kasar Sin na ci gaba da fadada, inda a watanni 6 na farkon shekarar bana, darajarsa ta kai kwatankwacin dalar Amurka biliyan 420. Kana kasar ta fitar da ayyukan ba da hidima da darajar su ta kai kudin Sin yuan tiriliyan 1.4.

A wannan gaba da kasar Sin ke gayyata sassan duniya su shiga a dama da su, a fannin bunkasa hada-hadar cinikayyar ba da hidima, sassan kasa da kasa na da wata dama mai kyau ta yin cudanya da koyi da juna, tare da nazarin fifikon da suke da shi a wannan muhimmin fanni. A hannu guda kuma, Sin za ta ci gaba da yayata manufar bunkasa ci gaba mai inganci a fannin, da kara bude kofa ga sassan waje, matakin da zai tabbatar da nasarar burin da ake da shi, na wanzar da daidaiton ci gaban tattalin arziki da walwalar al’ummar duniya baki daya. (Saminu Alhassan)