logo

HAUSA

Barawon da ke ihun kama barawo

2022-09-01 18:54:24 CMG Hausa

Daga Lubabatu Lei

Sinawa kan bayyana wanda ke neman dora laifinsa a kan wani a matsayin “barawon da ke ihun kama barawo”. Gaskiya kam, ’yan siyasar kasar Amurka ma sun amsa wannan suna.

Ga shi dai, kwanan nan ba da jimawa ba, Amurka ta sake “ihun kama barawo”, inda cibiyar GEC karkashin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta fitar da rahoton da ya zargi gwamnatin kasar Sin da neman shawo kan ra’ayoyin al’umma a game da jihar.

Amma gaskiyar lamari shi ne Amurka da ma sauran kasashen yamma su ne suke gurbata gaskiya da gurgunta fahimtar jama’a a kan abubuwan da ke faruwa a jihar ta Xinjiang, wandanda suka kawar da kai daga ci gaban tattalin arziki da zaman al’umma da aka cimma a jihar da ma yadda al’umma ’yan kabilu daban daban ke zaman walwala a jihar, kuma suka yi amfani da karfinsu ta fannin kafofin yada labarai, suka yada karairayin da suka shafi “kisan gilla” “aikin tilas” da sauransu a jihar Xinjiang, don cimma burinsu na dakile ci gaban kasar Sin bisa “batun Xinjiang”.

“Mun san cewa, babu wata matsala a Xinjiang, amma kirkiro matsalolin hakkin bil Adam na aikin tilas da kisan kare dangi, mataki ne mai amfani, don cimma burinmu na jefa gwamnatin kasar Sin cikin mawuyacin hali”, wannan shi ne furucin da jami’an diplomasiyya na kasar Amurka dake kasar Sin suka yi kwanan baya, lamarin da ya nuna ainihin abin da Amurka ke neman cimmawa.

Yayin da Amurka ke shafa mata bakin fenti, shin bai dace ba kasar Sin ta mayar da martani? Sai dai hakan ya zama “neman shawo kan ra’ayoyin al’umma a game da jihar Xinjiang” kamar yadda rahoton da Amurka ta fitar ya bayyana. Lallai Amurka ta amsa sunan “barawon da ke ihun kama barawo”.

Idan ba a manta ba, don neman kaddamar da yaki a Iraki, Amurka ta taba zargin Iraki din da mallakar makaman kare dagi bisa farin garin da ta nuna wanda ba a tabbatar da yanayinsa ba. Amurka tana yawan satar sauraron bayanan jami’an kasa da kasa, a yayin da kuma take zargin wasu da satar bayanai ta yanar gizo. Sai kuma a watan da ya gabata, kakakin majalisar wakilan kasar Amurka ta kai wata haramtacciyar ziyara yankin Taiwan na kasar Sin duk da rashin amincewar da kasar ta Sin ta nuna da kakkausar murya, daga bisani kuma ta zargi kasar Sin da “mayar da martanin da bai dace ba, wanda ya tsananta yanayin da ake icki a zirin tekun Taiwan.”

Mike Pompeo, tsohon sakataren harkokin wajen kasar Amurka ya taba bayyanawa a fili cewa, “Da karairayi da yaudara da sata duk muna yi, kuma muna shirya kwas na musamman a kan wannan.” Wannan ya kara tabbatar da cewa, Amurka za ta dauki duk matakin da ta ga dama don neman cimma burinta, kuma hakan ya kasance yadda take cudanya da kasa da kasa. (Mai Zane:Mustapha Bulama)