logo

HAUSA

Mamakon ruwan sama ya halaka mutane 82 a Jamhuriyar Nijar

2022-09-01 11:14:43 CMG Hausa

A jiya Laraba, ma’aikatar harkokin gidan Jamhuriyar Nijer, ta bayyana a wata sanarwa cewa, tun daga watan Yunin bana, ake sheka ruwan sama kamar da bakin kwarya a sassan kasar, inda ya zuwa yanzu, lamarin ya haddasa mutuwar mutane 82.

Sanarwar ta bayyana cewa, ruwan saman da ake ci gaba da shekawa a sassan kasar, ya yi sanadin rushewar gidaje. Ya zuwa ranar 29 ga watan Agusta kuma, mutane 82 ne suka mutu, baya ga mutane dubu 110 dake fama da bala’in, yayin da mutane 102 suka jikkata. Bugu da kari, lamarin ya haddasa babbar barazana ga sana’o’in kiwon dabbobi da shuke-shuke na kasar.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa, yankuna guda uku ne suka fi fama da wannan bala’i, wato yankin Maradi, da Zinder, da kuma Tahoua.

Yanayin damina a Jamhuriyar Nijar dai, yana farawa ne daga watan Yuli zuwa Satumba na ko wace shekara. A shekarar 2021, mutane 77 ne suka gamu da ajalinsu sakamakon bala’in ambaliyar ruwa a lokaci damina a Nijar, yayin da mutane sama da dubu 250 ne bala’in ya ritsa da su. (Maryam)