logo

HAUSA

Dakarun MINUSMA suna jigilar magunguna zuwa Gao yayin da 'yan ta'adda suka toshe babbar hanyar samar da kayayyaki

2022-09-01 10:03:45 CMG Hausa

Dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD dake kasar Mali (MINUSMA), sun yi jigilar muhimman magunguna zuwa cikin babban birnin Gao, bayan da 'yan ta'adda dauke da makamai suka tare babbar hanyar samar da kayayyaki dake yankin.

Stephane Dujarric, babban mai magana da yawun magatakardan MDD Antonio Guterres ya bayyana cewa, tawagar dake yankin ta sanar da cewa, za ta kai tan 1.5 na muhimman magunguna zuwa Gao a kowane mako, bisa bukatar hukumomin yankin, da nufin dakile tasirin karancin magunguna.

Dujarric ya shaidawa taron manema labarai da aka saba gudanarwa cewa, tun a watan Mayun da ya gabata ne, 'yan ta'adda suka tare babbar hanyar zuwa garin Gao.

Kakakin ya ce, tawagar MINUSMA tana kuma taimakawa a garin Douentza, inda dakarun wanzar da zaman lafiya na Togo suke duba lafiyar jama'a da kuma baiwa al'umma 450 jinya a wani asibitin tafi da gidanka.

Dujarric ya bayyana cewa, a Tin Hama da kauyukan da ke kewaye, inda tawagar ta kara daukar matakan tsaro don kare fararen hula, rundunar ba da agajin gaggawa ta kasar Jordan tana ba da taimakon jinya ga al'ummomin yankunan da iyalan da suka rasa matsugunansu, a wani mataki na samar da yanayi na tsaro da kariya. (Ibrahim Yaya)