logo

HAUSA

Darajar masana’antun samar da kayayyakin latironi na kasar Sin na karuwa cikin sauri

2022-08-31 10:29:04 CMG Hausa

Alkaluman da ma’aikatar masana’antu da fasahohin zamani ta kasar Sin ta gabatar jiya Talata sun nuna cewa, tsakanin watan Janairu da na Yulin bana, bangaren masana’antun samar da kayayyakin latironi masu alaka da fasahar sadarwa da na’urar kwamfuta na kasar na samun ci gaba cikin sauri, inda jimillar darajar karuwar manyan kamfanonin kera kayayyakin latironi ta karu da kashi 9.8%, idan an kwatanta da na bara.

A sa’i daya kuma, kamfanonin na kara fitar da kayayyakinsu zuwa kasashen ketare, inda adadin ya karu da kashi 7.1%, bisa makamancin lokacin bara.

Sa’an nan a fannin samun kudin shiga, manyan kamfanonin kasar Sin masu kera kayan latironi, sun samu kudin da yawansa ya kai Yuan biliyan 8290.7, kwatankacin dalar Amurka biliyan 1199.5, tsakanin watan Janairu zuwa watan Yulin bana, adadin da ya karu da kashi 7.9%, bisa na makamancin lokacin bara.

Wadannan alkaluma sun nuna wani yanayi mai kyau, wajen raya bangaren masana’antun samar da kayayyakin latironi masu fasahohin zamani a kasar Sin. Bayanai na cewa, zuwa yanzu, yawan kamfanoni masu kera kayayyakin latironi, ya kai fiye da dubu 164 a kasar. Daga cikinsu, sabbin kamfanonin da aka kafa tsakanin watannin Janairu zuwa Yulin bana sun kai fiye da 9340. (Bello Wang)