logo

HAUSA

An ceto mutane 8 yayin da wani gini ya rufta a Najeriya

2022-08-31 10:57:12 CMG Hausa

Rahotanni daga Najeriya na cewa, an yi nasarar ceto mutane 8, yayin da wasu da ba a san adadinsu ba, suka makale bayan da wani gini mai hawa uku ya rufta a jihar Kano ta Najeriya a ranar Talata.

Jami’in tsare-tsare na hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa reshen jihar Kano, Nuraddeen Abdullahi, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua ta wayar tarho cewa, wani gini mai hawa uku da ake ginawa, a wata shahararriyar kasuwa dake cikin birnin Kano, fadar mulkin jihar, ya ruguje a yammacin ranar Talata, inda ya rutsa da mutanen da ba a san adadinsa ba.

A cewar jami’in, ya zuwa yanzu, an yi nasarar ceto kimanin mutane 8, an kuma kai su asibiti domin duba lafiyarsu, yayin da ake ci gaba da aikin ceto wadanda suka makale a karkashin baraguzan ginin. (Ibrahim Yaya)