logo

HAUSA

Matakan Sin na bunkasa tattalin arziki mai inganci ba tare da gurbata muhalli ba

2022-08-31 09:34:01 CMG Hausa

Duk da rashin tabbas da kalubalen da tattalin arzikin duniya ke fuskanta, sakamakon annobar COVID-19 dake ci gaba da addabar sassan duniya, gwamnatin kasar Sin ta dauki managartan matakai na raya tattalin arziki mai inganci, ba kuma tare da gurbata muhallin duniyarmu ba. 

Daya daga cikin irin wadannan sun hada da sanya wasu manyan bankunan kasashen waje guda biyu dake nan kasar Sin wato, Deutshe Bank na kasar Jamus, da Societe Generale na kasar Faransa a cikin shirin gwamnatin kasar na rage fitar da iskar Carbon mai dumama yanayin duniyarmu yayin da ake raya tattalin arziki.

Karkashin wannan shiri da muhukuntan kasar Sin suka bullo da shi a watan Nuwamban shekarar da ta gabata, masu neman rance da ke fatan raya sana’o’insu, za su nemi kudade masu karamin kudin ruwa daga bankunan karkashin kulawar babban bankin al’umma na kasar Sin.

Wannan shiri zai samar da karin damammaki ga masu neman rance na ketare wajen shiga a dama da su a cikin shirin, da ma cin gajiya daga manufofin kasar Sin na rage fitar da iskar Carbon mai dumama yanayin duniyarmu.

Kasar Sin dai ta sanar da kaiwa ga kololuwar fitar da iskar Carbon kafin shekarar 2030, da daidaita fitar da iskar ta Carbon, kafin shekarar 2060. Rancen ci gaban ba tare da gurbata muhalli ba, ya kai kudin Sin Yuan Triliyan 15.9, kwatankwacin dalar Amurka triliyan 2.31. Karuwar kaso 33 cikin 100 kan na shekarar da ta gabata.

Bugu da kari, kasar Sin tana dora muhimmanci kan farfadowa ba tare da gurbata muhalli ba, da kara bude kofa ga kasashen waje, da nuna adalci da daidaito ga dukkan hukumomin kudi na gida da na waje, da taimaka musu wajen samun bunkasuwa bisa doka.

Wasu bayanai na nuna cewa, a cikin shekaru 5-8, an samu gagarumin ci gaba a fannin samarwa da biyan bukatu a tsarin laturori na kasar Sin, da inganta tashoshin samar da wutan lantarki, da na’urorin samar da makamashin da ake iya sabuntawa da aka kafa.

Bunkasuwa da juriyar tattalin arziki da babbar kasuwar kasar Sin, duk suna kara janyo ‘yan kasuwa daga kasashen waje. Wannan ya nuna yadda ake kara nuna imani kan managartan manufofin kasar game da raya tattalin arziki. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)