logo

HAUSA

Yadda bikin cinikayyar hidimomi ke jan hankalin ‘yan kasuwa

2022-08-31 20:30:16 CMG Hausa

Kwanan baya babbar manajar yankin masana’antun Jinchi na kasar Thailand Wanna lorluelert, ta gaya wa manema labarai cewa, “Bikin cinikayyar hidimomin kasar Sin yana amfanar da kowannenmu kai tsaye.”

Kawo yanzu yankin masana’antun Jinchi, ya riga ya halarci taron tattaunawa tsakanin kamfanoni ta kafar bidiyo, wanda bikin cinikayyar hidimomi na kasa da kasa na kasar Sin ya shirya har sau uku. Wanna ta kara da cewa, bikin ya taimake su matuka, yayin da suke neman ‘yan kasuwar kasar Sin, kuma a sanadin haka, karin kamfanoni sun shiga yankin masana’antunsu, tare da fasahohin zamani na kasar Sin.

Hakan ya nuna manyan sakamakon da bikin ya samu, wajen ingiza hadin gwiwar dake tsakanin kamfanonin kasa da kasa a cikin shekaru goma da suka gabata. Tun bayan shirya bikin a karo na farko a shekarar 2012, ya zuwa yanzu yana kara jan hankalin ‘yan kasuwa, har ya kai matsayin irinsa mafi girma a fadin duniya.

Yanzu haka an kaddamar da bikin na bana wato na shekarar 2022 a yau Laraba, inda ya samu halartar manyan kamfanonin kasa da kasa sama da 400 a zahiri, adadin da ya karu da kaso kusan 3 bisa dari, bisa bikin na bara.

An lura cewa, kasar Sin ta shirya bikin ne domin samar da damammaki ga kamfanonin ketare, domin su shiga babbar kasuwar kasar Sin. A sa’i daya kuma, ya samar da izini ga kamfanonin kasar Sin, yayin da suke amfani da kasuwar gidan kasar da kasuwar kasa da kasa.

Duk wadannan sun shaida babbar ma’anar bikin cinikayyar hidimomin kasa da kasa na kasar Sin, wanda shi ne babban sakamakon da kasar Sin ta samu, yayin da take kokarin bude kofa ga waje. (Jamila)