logo

HAUSA

Kwamitin Sulhu MDD ya sabunta takunkuman da aka kakabawa Mali

2022-08-31 10:36:31 CMG Hausa

Jiya ne, kwamitin sulhu na MDD ya sabunta dokar hana yin tafiye-tafiye da kwace kadarorin da aka kakabawa daidaikun mutane da hukumomin da ake zargi da hana aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya da sulhu a kasar, har zuwa ranar 31 ga watan Agustan shekarar 2023.

Kudiri mai lamba 2649 ya samu amincewar baki dayan mambobin kwamitin majalisar mai wakilai 15, tare da tsawaita wa'adin kwamitin kwararru da ke sanya ido kan aiwatar da takunkuman, har zuwa ranar 30 ga watan Satumban shekarar 2023, da kuma bukatar tawagar hadin gwiwa ta MDD dake Mali ta taimakawa kwararrun.

Majalisar ta kuma bayyana a cikin kudurin cewa, halin da ake ciki a kasar Mali, na ci gaba da zama barazana ga zaman lafiya da tsaron kasa da kasa a yankin.

Haka kuma majalisar ta bukaci kwamitin kwararrun, da ya fitar da rahoton tsakiyar wa'adi nan da ranar 28 ga watan Fabrairun shekarar 2023, da kuma rahoton karshe kafin ranar 15 ga watan Agustan shekarar2023, ya kuma rika sabuntawa a tsakani daga lokaci zuwa lokaci. (Ibrahim Yaya)