logo

HAUSA

Tattalin arziki mai nasaba da fasahar sadarwa ya bunkasa sosai a kasar Sin

2022-08-30 08:56:55 CMG Hausa

A cikin shekaru 10 da suka wuce, darajar tattalin arziki mai nasaba da fasahar sadarwa a kasar Sin ta karu zuwa kudin Sin RMB yuan triliyan 45.5 daga triliyan 11, kuma adadinsa a GNPn kasar ya karu zuwa 39.8% daga 21.6%.

A halin yanzu, daga birane zuwa yankunan karkara, daga al'umma zuwa ga daidaikun mutane, ci gaban intanet a kasar Sin ya kara samar da kuzari ga ci gaban tattalin arziki mai inganci.  (Tasallah Yuan)