logo

HAUSA

Rikici ya barke a zanga-zangar da aka gudanar a birnin Bagadazah

2022-08-30 21:47:25 CMG Hausa

Wani jami'in ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar Iraki ya bayyana a jiya Litinin cewa, rikicin da ya barke a zanga-zangar da aka gudanar a yankin Green Zone na birnin Bagadazah ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 12, tare da jikkata wasu gommai. Har wa yau, daga karfe uku da rabi na yammacin ranar, an fara aiwatar da dokar hana fitar motoci da al’umma daga gida a birnin.(Lubabatu)