logo

HAUSA

’Yan sandan Madagascar sun bude wuta kan masu zanga-zanga, inda a kalla mutane 11 suka mutu

2022-08-30 10:54:39 CMG Hausa

Rahotanni daga kamfanonin dillancin labarai na AP da AFP na cewa, kimanin mazauna Madagascar 400 ne suka gudanar da zanga-zanga a gaban ofishin 'yan sanda dake yankin, inda suka bukaci a sako wasu mutane hudu da ake zargi da sace kananan yara zabiya.

Daga bisani ne kuma 'yan sanda suka budewa masu zanga-zangar wuta, inda suka kashe a kalla mutane 11 tare da jikkata wasu da dama.

Shugaban kasar Madagascar ya wallafa a shafukan sada zumunta cewa, ya yi matukar bakin ciki da jin wannan labari, inda ya yi kira ga jama'a da su kwantar da hankalinsu tare da yin alkawarin gudanar da bincike kan lamarin.

Alkaluman da asusun tallafawa kananan yara na MDD (UNICEF) ya fitar a watan Maris na shekarar 2022 dake nuna cewa, a cikin shekaru biyu da suka gabata, an aikatar da laifuffukan yin garkuwa ko kai hare-hare, har ma kisan mutane masu fama da lalurar zabiya a fadin Madagascar fiye da sau 10. (Ibrahim Yaya)