Jakadan Habasha: A shirye Habasha take ta tattauna kan madatsar ruwan Nile bisa sanya idon AU
2022-08-30 10:52:49 CMG Hausa
Kasar Habasha ta bayyana cewa, a shirye take ta tattauna da kasashen Sudan da Masar, game da batun babbar madatsar ruwan kasar Habasha (GERD) a karkashin jagorancin kungiyar Tarayyar Afirka (AU).
Jakadan Habasha dake kasar Sudan Yibeltal Aemero, ya bayyana a yayin wani taron manema labarai a Khartoum, babban birnin kasar Sudan cewa, kasarsa na da yakinin za a iya warware dukkan batutuwa ta hanyar tattaunawa da yin sulhu.
Ya bayyana cewa, an yi nasarar kammala aikin cike babbar madatsar ruwar ta GERD kashi na uku, ba tare da cutar da Sudan ba ko kuma illa ga kasashen Sudan da Masar da kogin ya ratsa ba.
Ya kara da cewa, aikin cikewan ya rage illar ambaliyar ruwa a Sudan, duk da ikirarin da mahukuntan kasar suka yi a baya-bayan nan cewa, madatsar ruwan za ta yi mummunar illa ga 'yan kasar Sudan miliyan 20.
A ranar 12 ga watan Agusta ne, gwamnatin Habasha ta sanar da samun nasarar kammala kashi na uku na aikin cike babbar madatsar ruwan. (Ibrahim Yaya)