logo

HAUSA

Adalci shi ne tushen hadin gwiwa

2022-08-29 17:14:14 CMG Hausa

Yau Litinin ne aka kaddamar da bikin makon tinkarar sauyin yanayi a nahiyar Afirka na wannan shekara ta 2022, a kasar Gabon. Hakika batun sauyin yanayi na kara janyo hankalin jama’a, musamman ma ta yin la’akari da yadda ake samun abkuwar karin nau’o’in bala’u daga Indallahi a wurare daban daban.

A shekarar da muke ciki, kasashe da dama dake nahiyar Afrika, irinsu Madagascar,da Mozambique, da Malawi, sun fuskanci radadin wani nau’i na bala’u. Kana an gamu da matsalar ambaliyar ruwa a jihar Jigawa dake Najeriya, sai kuma jihohin Zinder, da Maradi, da Diffa a jamhuriyar Nijar. A cewar Akinwumi Adesina, shugaban bankin raya nahiyar Afirka, matsalar sauyin yanayin duniya, ta kan haddasa asarar dalar Amurka biliyan 7 zuwa 15 a kasashen Afirka, a duk shekara.

Don daidaita wannan matsala, kasashen duniya sun kudiri niyyar rage fitar da iska mai dumama yanayi, tare da kulla wasu yarjeniyoyi, inda aka tanadi cewa, kasashe masu sukuni da kasashe masu tasowa, za su dauki nauyin daidaita matsalar sauyin yanayi tare, sai dai ayyukan da za su dauki nauyin gudanarwa sun sha bamban. Wato ya kamata kasashe masu sukuni su rage fitar da iska mai dumama yanayi, da samar da kudade da fasahohi ga kasashe masu tasowa, yayin da kasashe masu tasowa ba dole ne a kayyade musu yawan iska mai dumama yanayi da za su rika fitarwa ba

Sai dai har zuwa yanzu, ba a aiwatar da wadannan ka’idojin da kyau ba. Maimakon haka, kasar Amurka da kasashen Turai, da sauran kasashe masu sukuni, suna neman ikon jagorantar ayyukan tinkarar sauyin yanayi a duniya, don neman danka wa kasashe masu tasowa nauyi na rage fitar da iskar dake dumama yanayi. Kana sau da yawa, kasashe masu sukuni sun kasa cika alkawarin da suka yi, na samar da a kalla dala biliyan 100 ga kasashe masu tasowa a duk shekara, don tallafawa aikin tinkarar sauyin yanayi. Haka zalika, kasar Amurka ta bullo da dabaru daban daban, ciki har da na siyasa, don neman shawo kan bangaren samar da kayayyaki masu alaka da rage fitar da iska mai dumama yanayi, yayin da kasashen Turai a nasu bangare, suna fakewa da batun tinkarar sauyin yanayi, wajen daukar matakan kariyar ciniki. Dukkansu sun fi karkata ga moriyar kai fiye da moriyar bai daya ta dan Adam.

Hakika dai, babu adalci a matakan kasashen Turai da kasar Amurka. Saboda tun kafin kasashe masu tasowa su fara raya masana’antu, kasashe masu sukuni na yammacin duniya, sun kwashe kimanin shekaru 200 suna kokarin raya masana’antu tare da fitar da iska mai guba. Kana yanzu haka kasashe masu tasowa, suna fitar da iska mai dumama yanayi ne sakamakon gudanar da masana’antu na samar da dimbin kayayyakin da kasuwannin kasashe masu sukuni ke bukata.

Ban da wannan kuma, kasashe masu tasowa, ba su da karfin daukar karin nauyin rage fitar da iska mai dumama yanayi. Haka wannan batu yake, musamman ma a kasashen Afirka. Kamar yadda wani shahararren masani mai suna Taling Rodrigue, dan kasar Kamaru, ya fada: galibin kasashen dake nahiyar Afirka na kokarin raya kayayyakin more rayuwa, da masana’antu, inda suke tinkarar kalubaloli da yawa, musamman ma a fannonin raya tattalin arziki, da karuwar yawan al’umma. Sai dai a lokaci guda suna zama karkashin tarnakin manufofin rage fitar da iska mai dumama yanayi, wadda ta kasance iri daya da ta kasashen yamma. Wannan yanayi ya sa kasashen Afirka kasa sauke nauyin da aka dora musu na rage fitar da iskar dake dumama yanayi.

Ganin haka ya sa kasar Sin da sauran kasashe masu tasowa ke daga murya a wurare daban daban, don yin kira ga gamayyar kasa da kasa da su bullo da tsarin aiki mai adalci, don tabbatar da tushen hadin gwiwar kasashen daban daban, a fannin tinkarar matsalar sauyin yanayin duniya. Muna jiran kasashen duniya, musamman ma kasashe masu sukuni na yammacin duniya, da su amsa wannan kira. (Bello Wang)