logo

HAUSA

Somaliya da hukumomin MDD sun habaka yin alluran rigakafin COVID-19 duk da farin da kasar ke fuskanta

2022-08-29 09:55:26 CMG Hausa

Somaliya da hukumomin MDD biyu, sun sha alwashin kara kaimin yin allurar rigakafin cutar COVID-19 a fadin kasar, a daidai gabar da ake fama da matsanancin fari da ke addabar sassan kasar.

Ma'aikatar lafiya ta Somaliya, da hukumar lafiya ta duniya (WHO), gami da asusun tallafawa yara na MDD ko UNICEF, sun bayyana cewa, wasu daga cikin kalubalen da ke hana allurar rigakafin COVID-19 a Somaliya, sun hada da takaita isa ga wasu yankuna saboda rashin tsaro ko kalubalen kayan aiki.

Wakiliyar UNICEF a Somaliya Wafaa Saeed Abdelatef ta ce, gwamnati ta samu ci gaba mai armashi wajen samar da allurar rigakafin COVID-19 masu tsaro da inganci.

Saeed ta bayyana cikin wata sanarwar hadin gwiwa da hukumomin suka fitar a Mogadishu, babban birnin Somaliya cewa, akwai bukatar yin alluran riga kafin COVID-19 da sauran ayyukan ceton rai, saboda yanayi na jin kai da ake ciki, musamman wadanda suka rasa matsugunansu, da yankunan karkara, da kuma makiyaya.

Ta ce asusun UNICEF zai ci gaba da yin aiki kafada da kafada da gwamnati da abokan hulda, domin tabbatar da ganin al’umma sun fahimci alfanun allurar rigakafin.

A cewar ma’aikatar lafiyar kasar, ya zuwa yanzu, kusan mutane miliyan 2.3 ne aka yiwa cikakken rigakafin cutar COVID-19, yayin da sama da mutane miliyan 1.9 ba su karbi rigakafin ba. (Ibrahim Yaya)