logo

HAUSA

Yang Ning: Ba da gudunmuwar kuruciya da karfi wajen farfado da yankunan karkara

2022-08-29 13:30:47 CMG Hausa

Yang Ning ta kasance ‘yar asalin Jiangmen, wani kauye a Rongshui mai cin gashin kansa dake Liuzhou na yankin Guangxi Zhuang mai cin gashin kansa na kudancin kasar Sin. A shekarar 2010, bayan ta kammala jami’a a Nanning babban birnin Guangxi, inda ta karanta fannin tafiyar da harkokin kasuwanci, ta koma Jiangmen domin aiki a matsayin jami’ar kauye. A yanzu, Yang ce daraktan kwamitin kauyen, kuma sakatariyar JKS reshen kauyen. Ta kuma sadaukar da kanta wajen raya mahaifarta tare da taimakawa wajen horar da matasan kauyen.  

A 2016, Yang Ning ta kammala wa’adinta na biyu a matsayin jami’ar kauyen Jiangmen. “Yang na da kirki, kuma dukkanmu na sonta. Muna fatan za ta ci gaba da zama a kauyen. Amma mun fahimci za ta fi samun ci gaba a babban birnin,” cewar wani mazaunin kauyen. Haka ma wata abokiyar karatunta, ta yi kokarin shawo kanta don ta yi aiki a birni.

Sai dai, Yang ta zabi ta zauna, ta kuma ci gaba da aiki a Jiangmen. Ta ce, “ina jin na yi sa’ar rayuwa a wannan zamani, kuma a ganina, girmamawa ce shiga cikin gagarumin aikin yaki da talauci. Ba za a taba fahimtar yadda nake alfahari da zabi mai kyau da na yi, da abun da nake aiwatarwa ba. Ana bukatar matasan da suke da basira da dabaru a yankunan karkara.”

Yang ba ta taba daina laluben hanyoyin samar da karin kudin shiga ga mutanen kauyen ba. Bisa aminta da suka yi da ita, an sake zabar Yang a matsayin daraktar kwamitin kauyen a 2017. Ita ce mace ta farko da ta kammala jami’a, da ta zama daraktar kwamitin kauye a gundumar Rongshui da take ciki. An kuma zabe ta matsayin mataimakiyar wakilin jama’a na gundumar a wannan shekara.

Kankanar da ake nomawa a kauyen na da zaki, kuma ana sayen su sosai. Yang ta taimakawa matan kauyen kafa wata kungiyar hadin gwiwa. A watan Agustan 2018, kungiyar mata ta Rongshui ta shirya wani bikin girbin kankana a kauyen Jiangmen. “kankanarmu na da inganci sosai kuma suna samun karbuwa sosai a kasuwa. Yang na da kwarewa, muna alfahari da farin ciki,” cewar daya daga cikin matan, yayin bikin.

A shekarar 2020, Yang ta mika kudurin gyaran babban titin kauyen. A watan Junairun 2021 kuma, aka gyara titin, karkashin goyon bayan gwamnatin karamar hukumar.

“A baya, sai mun dauki taki a bayanmu ko kafada mun hau tsaunika, inda muke noman kankana. Yanzu kuwa, muna iya zuwa a mota, cikin sauki muke sufurin taki da kankana. Mun fi samun sauki a yanzu fiye da da,” cewar Zhang Haihui, wata mutuniyar kauyen. An kuma kafa fitilun a kan titin, masu amfani da hasken rana guda 237.

“A 2020, mun karfafawa wasu mutane gwiwar noman wani nau’in laimar kwado, kuma sun samu girbi mai armashi. A shekarar 2021, karin mutane suka shiga cikin noman, don haka sai muka fadada shirin na noman laimar kwado,” cewar Yang Ning.

Dong Yanfang, wata ‘yar kauyen ta furta cewa, “da karfafawar Yang, na noma laimar kwado a shekarar 2020, kuma na samu dubban kudade a shekarar. Na fara nomansa ne a bara.”

Wasu nau’ikan laimar kwado da ake ci, abubuwa ne na musammam da ake nomansu a yankunan kabilar Miao. A baya, mutane da dama na jan kafa wajen noman wadannan abubuwa, saboda wahalar sayar da su.

A 2016, Yang ta yanke shawarar sayar da kayayyakin amfani gona domin tallata al’adun da cimaka masu dadi na kabilar Miao, ta kafar intanet.

Yang, tare da wasu jami’ai 6, sun kafa wata cibiyar sayar da amfanin gona ta intanet, kuma suka bude shafi a manhajar Wechat, ta yadda za su rika tafiyar da kasuwanci ta intanet.

Sai suka fara sayar da kunshin cimaka ta intanet. Daga sannan kuma, matasan kauyen da dama suka koma Jiangmen daga birane, domin aiki a cibiyar.

A 2020, saboda kokarin Yang da mutanen kauyen, Jiangmen ya fita daga kangin talauci. Yanzu, masana’antu da dama na gudanar da ayyukansu a kauyen, kuma ababen more rayuwa a kauyen, da muhalli da yanayin zamantakewar jama’a, duk sun kyautatu matuka.

“Manufofin JKS da jami’an jam’iyyar ne suka haifar da kyautatuwar rayuwar mutanen kauyen,” cewar wasu mutane a kauyen. A watan Nuwamban 2020, aka zabi Yang matsayin sakatariyar reshen jam’iyya na kauyen.

Yang ta samu lambobin yabo da na karramawa da dama saboda gudummuwarta ga ci gaban yankin karkara a kasar Sin. Daga cikinsu akwai na Mace mafi jajircewa ta duk fadin kasar Sin, da na yaki da talauci, da na matasa mafiya nagarta na kasar. Haka kuma, Yang wakiliya ce ta majalisar mata ta kasa karo na 12.

“Burina shi ne, hidimtawa mutanen kauyen, kuma shi ne ma’anar rayuwata. Ina fatan karin matasa za su bayar da gudunmuwar kuruciya da karfinsu, wajen farfado da yankunan karkara,” cewar Yang Ning.(Kande Gao)