logo

HAUSA

Lardin KwaZulu Natal na Afrika ta Kudu na neman kara hada gwiwa da takwarorinta na BRICS

2022-08-29 10:36:46 CMG Hausa

Lardin KwaZulu Natal na Afrika ta Kudu, na neman aiwatar da shirye-shiryen musaya a bangarorin wasanni da al’adu da kasuwanci da ilimi da kasashen kungiyar BRICS.

Firimiyar lardin Nomusa Dube-Ncube ce ta bayyana hakan jiya, a lokacin da take jawabi da taya ‘yar tseren kasar Rasha, Alexandra Morozova murnar lashe tseren na ajin mata na 2022, a filin wasa na Moses Mabhida dake birnin Durban.

A cewarta, bangarorin yawon bude ido da na tattalin arziki da ma kananan harkokin kasuwanci na Lardin KwaZulu Natal, sun amfana daga gasar, tana mai tunatar da cewa, lardin ne ya karbi bakuncin taron BRICS na shekarar 2013, kuma tana son karin hadin gwiwa da kasashen BRICS.

Firimiyar na mayar da hankali ne musammam kan karfafa gwiwar aiwatar da shirye-shiryen musaya da za su amfanawa al’ummar lardin na KwaZulu Natal.

Ana daukar birnin Durban na Afrika ta Kudu da Guangzhou, babban birnin lardin Guandong na kasar Sin a matsayin tagwaye. Haka kuma, yankin birnin Ethekwini da ya kunshi Durban, na matsayin ‘yar uwa ga birnin Xiamen na lardin Fujian dake gabashin kasar Sin. (Fa’iza Mustapha)