logo

HAUSA

Algeria da Faransa sun bayyana aniyar su ta kyautata dangantaka

2022-08-28 17:35:49 CMG Hausa

Shugaban Faransa Emmanuel Macron, da takwaransa na Aljeriya Abdelmadjid Tebboune, sun bayyana aniyar su, ta bude sabon babin huldar kasashen su, yayin da shugaban Faransa ke kawo karshen ziyarar aiki ta yini uku a Aljeriya.

Hakan na zuwa ne, kasa da watanni 2, bayan da Aljeriya ta gudanar da bikin cika shekaru 60 da samun ‘yancin kai, bayan Faransa ta mulki kasar tsawon shekaru 132, da kuma mummunan yakin kwatar ‘yanci na shekaru 8 wanda ya daidaita kasar.

Kaza lika shirin kyautata alakar kasashen biyu, na zuwa ne a gabar da manyan kasashen Turai ke fadi-tashin maye gurbin makamashin da suke samu daga Rasha, da na kasashe irin su Aljeriya, wadda ke kan gaba a nahiyar Afirka wajen fitar da iskar gasa. Cikin hadaddiyar sanarwar da suka sanyawa hannu a jiya Asabar, shugabannin biyu sun amince da bude sabon babin sahihiyar dangantaka, ta hanyar kafa ginshiki mai nagarta, wanda zai maida hankali ga gina rayuwar matasa a nan gaba.

Kafin wannan lokaci, dangantaka tsakanin Faransa da Aljeriya ta yi tsami, inda a shekarar bara, lokacin da shugaban Faransa ya musanta wanzuwar kasar Aljeriya gabanin mamayar Faransashugaban Faransa, tare da zargin mahukuntan Aljeriya da furta kalaman nuna kiyayya ga Faransa, wanda hakan ya sanya Aljeriya janye jakadanta daga Faransa. (Saminu Alhassan)