logo

HAUSA

Dauki ba dadi tsakanin sassa masu adawa da juna a Libya ya hallaka mutane 23 da jikkata 140

2022-08-28 17:21:54 CMG Hausa

Rahotanni daga ma’aikatar lafiya ta kasar Libya na cewa, fafatawar da dakaru masu adawa da juna ke yi a sassan tsakiyar birnin Tirabulus, ta sabbaba kisan mutane 23, tare da jikkata karin wasu 140.

Ma’aikatar ta yi kira ga sassan dake dauki ba dadi, da su kaucewa kai farmaki kan asibitoci, duba da yadda tuni aka lalata wasu cibiyoyin kula da lafiya da asibitocin dake birnin, yayin da kuma jami’an lafiya suka rasa ikon kai dauki, ga marasa lafiya dake bukatar kulawar gaggawa a sassan birni.

Fada ya barke ne tun daga daren ranar Juma’a, tsakanin dakaru masu goyon bayan tsagin ‘yan majalissun wakilan kasar daga gabashi, da tsagin gwamnatin hadin kan kasa mai samun goyon bayan MDD. Tsagin na ‘yan majalissar wakilai sun janye goyon bayan su, ga jagorancin shugaban gwamnatin hadin kan kasar Abdul-Hamed Dbeibah, inda suka amince da kafa sabuwar gwamnati a watan Maris, karkashin jagorancin Fathi Bashagha zai jagoranta.

Game da hakan, wata sanarwa da kakakin babban magatakardar MDD Stephane Dujarric ya fitar a jiya Asabar, ya ce babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya damu matuka, bisa barkewar sabon tashin hankali a Libya. Mr. Guterres ya kuma yi kira ga sassan biyu, da su gaggauta dakatar da bude wuta a birnin Tirabulus. Yana mai fatan za su koma teburin shawarwari, domin warware bambancin siyasa dake tsakanin su, su kuma kaucewa amfani da karfin tuwo wajen warware sabani. (Saminu Alhassan)