logo

HAUSA

Iran da Najeriya sun rattaba hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwa a fannin makamashi

2022-08-28 17:18:01 CMG Hausa

Kasashen Iran da Najeriya, sun rattaba hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwa a fannin samar da makamashi. Sashen watsa bayanai na ma’aikatar albarkatun man kasar Iran ko Shana a takaice, shi ne ya labarta hakan, yana mai cewa, an kulla yarjejeniyar ne a gaban ministan ma’aikatar albarkatun man Iran Javad Owji, da karamin ministan mai na Najeriya Timipre Sylva.

Da yake tsokaci game da ci gaban, a gefen tattaunawar da suka yi da Mr. Sylva, Javad Owji, ya ce takardun da aka sanyawa hannu na kunshe da tanadin shigar da kwararru, da injiniyoyin Iran zuwa Najeriya. Kaza lika kasar za ta rika shigar da sinadarin urea zuwa Najeriyar.

Bugu da kari, Iran ta amince ta yi wa wasu matatun mai na Najeriya kwaskwarima, tare da gina wasu sababbi. Kuma bisa la’akari da dumbin albarkatun mai da iskar gas da Najeriya ke da su, Iran na fatan fadada hadin gwiwa da kasar a wannan fanni cikin tsawon lokaci mai zuwa.

A nasa bangare kuwa, Sylva ya ce Najeriya na fatan amfana daga fasahohin kasar Iran, na cin gajiya daga iskar gas, da gyara, da gina karin matatun mai a kasar, tare da kula da wadanda ke aiki yanzu haka a kasar. Har ila yau, Iran za ta bunkasa tsarin cin moriya daga fannin hako danyen mai da iskar gas, da kuma shigar da sinadarin urea Najeriya. (Saminu Alhassan)