logo

HAUSA

Nan gaba kadan bil adama zai rika amfani da mutum mutumin tallafawa gabban jiki

2022-08-26 14:13:29 CRI

Sanya sassan mutum mutumi, ko rigar mutum mutumin da ke iya taimakawa bil adama motsa gabban sa yadda ya kamata, abu ne da a baya ake gani a fina finai kawai, amma ga alama nan gaba kadan wannan fasaha za ta zamo gaskiya.

Sassan mutum mutumi da aka baje kolin su yayin taron karawa juna sani, albarkacin ranar mutum mutumin inji ta duniya ta shekarar 2022, wanda aka gudanar a ranar 18 zuwa 21 ga watan nan a birnin Beijing, sun karfafa gwiwar masu wasannin motsa jiki dake da wata nakasa ta gabbai, wajen samun fatan yin amfani da gabban su yadda ya kamata.

Cikin irin wadannan sassan mutum mutumi, akwai bangarorin da ake makalawa a bangarorin jikin mutum, domin baiwa gabobin kariya. Akwai nau’oin su da jami’ar Beihang ta kera, domin tallafawa mutane da wani barin jikin su ya shanye, ta yadda za su samu farfadowa daga cutar.

Masu bincike suna amfani da fasahar kwaikwayon tunanin bil adama ko AI a takaice, wajen tsara na’urorin mutum mutumi daidai da bukatar wanda zai yi amfani da su, inda ake samar da wani nau’i na riga mai dauke da na’urar dake bin tunanin mai sanye da ita, domin ta taimaka masa aiwatar da abubuwan da ya yi niyyar yi.

Irin wadannan mutum mutumi na bibiyar nufin mai amfani da shi. Misali a yayin tafiya, yana iya bin tunanin mutum game da ko yana son yin sauri ne ko kuma tafiya a hankali, sai na’urar ta taimaka masa yin hakan cikin sauki.

Da yake karin haske kan hakan, daraktan cibiyar gwaje gwaje na kirar mutum mutumin inji a jami’ar Beihang Shuai Mei, ya ce "Bayan lura da yanayin wuri, mutum mutumin na taimakawa mai amfani da shi wajen hawa sama, ko sauka kasa daga kan bene. Sassan mutum mutumi na iya taimakawa mai sanye da shi karfafa kwanjin jikin sa, da taimakawa motsin jikin mai fama da shanyewar barin jiki. An yi bincike da gwajin wannan fasaha, tare da masu fama da wannan cuta, an kuma tattara bayanai da sakamakon gwaje gwajen da aka yi. An gano yadda za a iya sarrafa irin wadannan na’urori na mutum mutumin inji yadda ya kamata". An gabatar da nau’in mutum mutumin inji kirar kasar Sin, tare da gwajin aiki da shi yayin tseren ‘yan wasa da dama da aka gudanar, a gasar Olympics ta birnin Beijing ta shekarar 2022 ajin nakasassu ko Paralympic”.

Shao Haipeng, sanye da wannan nau’i na sassan mutum mutumi, na cikin mutum 9 da suka kewaya da wutar fitilar Olympic a harabar “Temple of Heaven”, a ranar 2 ga watan Maris na shekarar 2022. Kafin hakan, Shao ya gamu da hadari ne, wanda ya haifar masa da karaya a kashin baya tun a shekarar 2017, kuma tun daga lokacin ba ya iya tsayuwa ko tafiya.

Tare da abokin wasan sa Li Tao, Shao ya kammala tseren gudun yada kanen wani, da taimakon sassan mutum mutumi da ake sanyawa a gabban jiki.

‘Yan wasan sun kammala tseren kilomita 42.2, cikin kwanaki 11, inda suka fara tsere daga garin Kezilesu Kirghiz na jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kai dake arewa maso yammacin kasar Sin, suka kuma kammala tseren a birnin Nanjing na lardin Jiangsu a ranar 25 ga watan Nuwambar shekarar 2018. Ita ma wata mai bukatar musamman mai suna Yang Shuting, ta shiga tseren na karba karba a ranar 4 ga watan Maris da taimakon wannan fasaha.

Yang ta gamu da hadarin mota ne a shekarar 2011. Kuma bayan watanni 5 tana samun horo, ta samu zarafin mikewa da yin tafiya, da taimakon kafafun mutum mutumi da take sanyawa.

Baya ga masu fama da shanyewar barin jiki, irin wadannan na’urori na taimakawa masu lafiya ma wajen daga abubuwa masu nauyin gaske.

Kamfanin “Atoun Model Y” ya kera wata nau’in rigar na’ura da ake sanyawa, wadda za ta iya taimakon mutum, ya daga karin nauyin da ya kai kilogiram 9, domin masu ayyukan karfi.

Kamfanin ya samar da irin wadannan sassan mutum mutumi da ake sakawa a jiki, an kuma yi amfani da su a filayen jirgin sama da kuma lokacin gasar Olympic, da Paralympic ta birnin Tokyo a shekarar 2020, inda ma’aikata suka rika amfani da su wajen daukar kayayyaki masu nauyi da sauya musu wuri.

Ta hanyar amfani da fasahohin AI, sassan mutum mutumi da ake samarwa za su kara taimakawa bil adama, da damammakin amfani da gabban sa, tare da share fagen gina rayuwa mai kyakkyawar makoma, ta amfani da sassan mutum mutumi tsakanin mutane.