logo

HAUSA

Yusuf Buba Yakub ya yaba da matakan da kasar Sin ta dauka na taimaka wa Afirka

2022-08-26 11:17:12 CMG Hausa

Shugaban kwamitin kula da harkokin waje na majalisar wakilan Nijeriya, Yusuf Buba Yakub, ya bayar da sanarwa a kwanan baya, inda ya bayyana cewa, yadda ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya sanar da soke basussuka 23 da kasar ke bin wasu kasashen Afirka 17 ba tare da kudin ruwa ba, ya kasance wani karin matakin yabawa tun bayan shekarar 2000.

Mr.Wang Yi ya sanar da hakan ne, lokacin da yake halartar taron masu aikin tabbatar da sakamakon da aka cimma, a taron ministoci karo na takwas na dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka. Ya kuma kara da cewa, zuwa shekarar 2019, gaba daya, gwamnatin kasar Sin ta soke basussukan da take bin kasashen Afirka, da suka kai dalar Amurka biliyan 3.4, matakin da ya shaida dankon zumuncin da ke tsakanin Sin da al’ummar Afirka.

Yusuf ya ce, baya ga soke basussukan da take bin kasashen Afirka, kasar Sin tana kuma ta kara shigar da kayayyaki daga kasashen Afirka, inda ta amince da kasashen Afirka su fitar da kayayyakinsu zuwa Sin ba tare da sanya musu kudin kwastan ba, don tallafa wa kasashen Afirka ta fannonin bunkasa ayyukan gona da na kere-kere, tare da kuma fadada hadin gwiwarta da kasashen Afirka, ta fuskokin tattalin arzikin zamani, da kiwon lafiya, da kiyaye muhalli da sauransu. Ya ce wadannan matakai da gwamnatin kasar Sin ta dauka a jere matakan diplomasiyya ne na sada zumunta, wadanda suka samar da misali ga sauran kasashen duniya.  (Lubabatu)