logo

HAUSA

Ana fargabar asarar rayuka sakamakon ruftawar wani gini a babban birnin Najeriya

2022-08-26 20:30:10 CMG Hausa

Rahotanni daga Najeriya na cewa, wani gini mai hawa uku da ake kan ginawa a wata unguwa da ke wajen birnin Abuja, fadar mulkin Najeriya, ya ruguje da sanyin safiyar Juma’ar nan, ba tare da sanin adadin mutanen da suka makale a ciki ba.

Mai magana da yawun hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasar (NEMA) Ezekiel Manzo, ya bayyana cewa, an yi nasarar ceto a kalla mutane hudu da suka samu raunuka daga baraguzan ginin, wanda ba zato ba tsammani ya rufta da sanyin safiyar yau, a lokacin da ake ruwan sama a Kubwa, wani yanki da ke wajen Abuja, babban birnin kasar.

Manzo ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua ta wayar tarho cewa, har yanzu akwai mutanen da suka makale, kuma ana ci gaba da gudanar da aikin ceto. (Ibrahim)