logo

HAUSA

Duniya ba ta bukatar duk wani nau’i na yakin cacar baka

2022-08-25 16:32:40 CMG Hausa

A baya bayan nan, yayin zaman kwamitin tsaro na MDD game da rikicin kasar Ukraine, an tabo muhimman batutuwa game da halin da ake ciki, don gane da wannan rikici da ya ki ci ya ki cinyewa, wanda a yanzu haka ya doshi wata na 7.

Tuni sassan duniya daban daban suka dandani radadin tasirin wannan rikici, kama daga kamfa, da hauhawar farashin makamashi a sassan nahiyar Turai, zuwa karancin hatsi, da takin zamani da sassan kasashe masu tasowa, kamar nahiyar Afirka ke fama da shi.

Game da wannan batu, tsagin kasar Sin na ganin a wannan gaba da duniya ke fuskantar manyan kalubale, ciki har da yunkurin farfadowa daga tasirin annobar COVID-19, ba wata kasa a duniya dake fatan sake fuskantar yakin cacar baka.

Hakan na nufin kasar Sin ba ta gamsu da yadda wasu kasashen duniya, musamman masu karfin fada a ji ke kara rura wutar rikice-rikice, da haifar da sabani a sassan duniya daban daban ba. Kaza lika matakin kungiyar tsaro ta NATO, na kara fafada tasirinta zuwa gabashin duniya, bai haifar da komai ba illa fito na fito da rura wutar rikici.

Kasar Sin ta gamsu cewa, yanayin matsi da ci gaban duniya ke fuskanta, ya wajabta yin taka tsantsan, da zage damtse, wajen ganin an kawar da rarrabuwar kawuna, da kaucewa rikici tsakanin sassan kasa da kasa.

Irin yadda kasashe masu tasowa suke fama da kamfar hatsi sakamakon rikicin Rasha da Ukraine, ya nuna cewa, zaman lafiyar wasu yankunan duniya, na iya yin babban tasiri ga sauran yankuna, kuma abu mafi dacewa shi ne sassan kasa da kasa su yi hadin gwiwa da juna, wajen kawo karshen duk wasu matakai na rura wutar cacar baka, wadda sau da yawa ke kaiwa ga barkewar tashe-tashen hankula. (Saminu Hassan)