logo

HAUSA

Jakadan Sin dake Nijar ya ziyarci filin wasan motsa jiki na Janar Seyni Kountche

2022-08-25 11:48:43 CMG Hausa

Jakadan kasar Sin da ke Jamhuriyar Nijar Jiang Feng, da ministan matasa da wasannin motsa jiki na kasar Sékou Doro Adamou, sun ziyarci filin wasan motsa jiki na Janar Seyni Kountche, wanda aka gina shi bisa taimakon kasar Sin.

Yayin ziyarar, jakada Jiang Feng, ya zanta da manema labarai, inda ya bayyana cewa, filin wasannin motsa jiki na Janar Seyni Kountche, wata alama ce ta birnin Yamai, kana alama ce dake shaida zumuncin da ke tsakanin Sin da Nijar, da hadin gwiwar kasashe masu tasowa, wanda ke ba da babbar gudummawa ga ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al’ummar Nijar. 

Jakadan Jiang ya jaddada cewa, an riga an shigar da aikin gyara filin wasan motsa jikin, cikin manyan ayyuka 9, da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar, a yayin taron ministoci karo na 8 na FOCAC. Kuma kasar Sin na son yin kokari tare da Nijar, wajen raya kyakkyawar makomar bai daya a tsakanin ta da Nijar, da ma dukkanin nahiyar Afirka a sabon zamanin da muke ciki.

A nasa bangaren kuwa, minista Adamou cewa ya yi, kasarsa na matukar godiya bisa goyon bayan da Sin ke nunawa sha’anin wasannin motsa jikinta. Ya ce ba don wannan goyon baya ba, da Nijar ba ta cimma nasarar samu babban filin wasanni irin wannan ba. Kaza lika al’ummar kasar musamman matasa, ba za su more yanayi mai dadi irin wannan ba.

Adamou ya kara da cewa, hadin kai a tsakanin Nijar da Sin ya kasance na a zo a gani. Kuma Nijar na mai da Sin a matsayin aminiyar hadin kai bisa manyan tsare-tsare, tana kuma fatan za a inganta hadin gwiwarsu a fannoni daban daban, musamman a fannonin kula da matasa da wasannin motsa jiki, a kokarin daga dangantakar hadin kai ta aminci tsakaninsu zuwa matsayi na gaba.  (Kande Gao)