logo

HAUSA

Jakadan Sin da ke Najeriya ya gana da ministan harkokin wajen kasar

2022-08-25 11:45:43 CMG Hausa

 

Jakadan kasar Sin da ke Tarayyar Najeriya Cui Jianchun, ya gana da ministan harkokin wajen kasar Geoffrey Onyeama a jiya Laraba, inda suka yi musanyar ra’ayoyi kan ci gaban dangantakar da ke tsakanin bangarorin biyu.

Yayin ganawar ta su, sun waiwayi kyawawan sakamakon da kasashen biyu suka samu a fannonin amincewar siyasa, da hadin kan tattalin arziki da cinikayya, da hadin gwiwar tsaron ayyukan soja, da daidaituwar harkokin kasa da kasa, da ma cudanyar al’adu. Kana bangarorin biyu sun amince da kara azamar aiwatar da babban tsarin neman cigaba na 5GIST, a karkashin inuwar kwamitin kula da harkokin gwamnatocin biyu, a kokarin samun karin sakamakon hadin kansu, ta yadda za a kara cin moriya daga jituwar da ke tsakanin Sin da Najeriya. (Kande Gao)