logo

HAUSA

Sai An Sha Wuya A kan Sha Dadi

2022-08-24 16:56:02 CMG Hausa

Sanin kowa ne cewa, duk kasar dake fatan samun ci gaba har ma a rika jin amonta a duniya, wajibi ne al’ummarta su zage damtse wajen ganin wannan buri ya tabbata. Kamar sauran al’ummomin kasashen duniya, al’ummar Sinawa sun hada karfi da karfe wajen gina kasar Sin mai bin tsarin gurguzu mai sigar musamman ta kasar Sin a sabon zamani.

Gagarumin ci gaban da kasar Sin ta cimma a cikin shekaru 10 da suka gabata (2012-2022), sun hada da fannonin tattalin arziki, da binciken sararin samaniya, da fannin kirkire-kirkire da inganta muhalli da zaman rayuwar jama’a da sauransu. Bayanai na cewa, karfin tattalin arzikin kasar Sin ya kai wani sabon matsayi, ma’aunin GDPn kasar ya kai Yuan triliyan 114, adadin da ya kai kashi 18 bisa dari na karfin tattalin arzikin duniya, wanda bai wuce kashi 11.4 bisa dari ba a shekarar 2012. Masu iya magana na cewa, idan ka ga wane ba banza ba.

A wadannan shekaru, kasar Sin ta ba da gudummawar kashi 30 bisa dari ta fuskar bunkasuwar tattalin arzikin duniya, wadda ta kasance babbar kasar dake taimakawa karuwar tattalin arzikin duniya. Kana ta yi nasarar warware babbar matsalar fama da kangin talauci, wadda ta damu jama’ar Sin cikin dubban shekaru a baya.

Yanzu haka, akwai mazauna kauyuka kimanin miliyan 98.99 da suka yi ban kwana da kangin talauci. Adadin kauyukan da suka sauya zuwa birane, ya karu daga 53.1% zuwa 64.7%. Mazauna kauyuka kimanin miliyan 180 sun kaura zuwa birane. 

A matsayinta na kasar dake kan gaba wajen yawan masu amfani da intanet a fadin duniya, kuma daya daga cikin bangaren da kasar ta samu gagarumin nasara, kasar Sin na kan hanyar sauyawa daga yawan adadi zuwa raya harkar intanet mai inganci, da gina tsarin tafiyar da yanar gizo mai cike da tsaro, sakamakon kyautatuwar ababen more rayuwa masu inganci, da ci gaban fasaha da bunkasar tattalin arziki na zamani. Hakika kasar Sin ta ciri Tuta.

Tsakanin wadannan shekaru da muke batu, adadin masu amfani da yanar gizo a kasar Sin, ya karu daga miliyan 564 zuwa fiye da biliyan 1.03, abin da ya sanya ta zama matsayi na daya a duniya. Kasar Sin ta samar da manyan hanyoyin sadarwa na 5G da layin fiber optic mafi girma a duniya. Kuma duniya ta shaida wannan nasara.

Darajar tattalin arzikin zamani na kasar Sin, ta tashi daga kudin Sin RMB yuan tiriliyan 11 kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan 1.6 a shekarar 2012 zuwa yuan tiriliyan 45.5 a shekarar 2021, wanda ya sanya ta ci gaba da zama kasa ta biyu a duniya a cikin shekaru da dama a jere.

Yawan jimillar tattalin arzikin zamani a GDPn kasar, shi ma ya karu daga kashi 21.6 cikin 100 a shekarar 2012 zuwa kashi 39.8 cikin 100 a shekarar 2021. Hada-hadar cinikayyar Intanet ta kasar Sin da tsarin biyan kudi ta wayar salula, duk sun kasance a kan gaba a duniya. Nasarorin da kasar Sin ta cimma a fannoni daban-daban, a wadannan shekarun da suka gabata, ba nasara ce kawai ga kasar Sin kadai ba, nasara ce ga duniya baki daya. Hakan ya kara jaddada cewa, sai an zubar da ruwa a kasa kafin a taka damshi. (Ibrahim Yaya)