logo

HAUSA

Ya Wajaba Amurka Ta Kaucewa Sake Maimaita Irin Kuskuren Da Ta Aikata Game Da Taiwan

2022-08-24 10:54:18 CMG HAUSA

DAGA CMG HAUSA

A duniyar yau, ba wanda ya zarce Amurka a fannin iya maida fari baki, da juyar da tunanin al’umma. Kasa ce dake kan gaba wajen ta da husuma, da kin karbar kuskuren ta, da sauya matsaya da cin dunduniya, halayen da suka zamewa kasar dabi’a a duk lokacin da take cudanya da sassan kasa da kasa. To sai dai kuma, karya ba za ta tserewa gaskiya ba. Idan an kalli batun da ya shafi takaddamar zirin Taiwan, duk mai hankali zai fahimci abu ne da Amurka ta tsara domin yin tsokana.

Bisa nufinta na tabbatar da daidaito a zirin Taiwan, tun da wuri Sin ta bayyana rashin amincewa, da shirin ziyarar kakakin majalissar wakilan Amurka Nancy Pelosi, kasar Sin ta yi ta nanata mummunar illar da ziyarar ta Pelosi za ta haifar, da ma sakamakon da Amurkar za ta samu idan har Pelosi ta aiwatar da ziyarar, duk da kashedin da ya fito daga sassa daban daban.

Dokokin kasa da kasa, sun baiwa kasashe ikon mulkin kai da tsaron yankuna, kana sun haramtawa duk wata kasa tsoma baki cikin harkokin cikin gidan wata. Don haka, bisa kunnen kashe da Amurka ta yi, ta aikata mummunar ta’asa, kuma Sin ba ta da zabi, illa ta mayar da martani.

Matakai daban daban da kasar Sin ta aiwatar domin mayar da martani ga waccan ziyara, na da nufin yin gargadi ne ga masu aikata ta’asa, ta yunkurin samar da ’yancin Taiwan. Sin ta zartas da matakan kare babbar moriyarta bisa doka. Kuma matakan nata sun dace da dokokin kasa da kasa da na cikin gida.

Tun fil azal, yankin Taiwan bangare ne na kasar Sin. Kuma sakamakon tsokana daga waje, ya sa dakarun sojin kasar Sin suka gudanar da atisayen soji, da sarrafa makamai a yankunan tekun dake daura da tsibirin na Taiwan, a wani mataki na tabbatar da ikon mulkin kai, da tsaron yankunan Sin. Wannan kuma na kunshe ne cikin tanade-tanaden kundin mulkin kasar, da dokokin dake haramta yunkurin ballewa daga kasar, da ma sauran dokoki masu nasaba da hakan.

Manufar kasar Sin daya tak a duniya, muhimmiyar ka’ida ce da kasar Sin ke karewa. Don haka ya wajaba, Amurka ta koyi darasi daga matakin kuskure da Pelosi ta aikata, ta komawa hanya madaidaiciya, wadda za ta dace da manufar kasar Sin daya tak a duniya, da sanarwoyi 3 da sassan biyu suka sanyawa hannu. Ya wajaba Amurka ta kaucewa kara yin wasu kura-kurai. Idan kuma ta ci gaba, Sin za ta maida martani yadda ya kamata. (Saminu Alhassan)