logo

HAUSA

Wasu ayyuka tara za su bunkasa ci gaban hadin gwiwar Sin da Afrika ta kowacce fuska

2022-08-24 20:08:09 CMG Hausa

Mataimakiyar shugaban hukumar Tarayyar Afrika (AU) Monique Nsanzabaganwa, ta ce wasu ayyuka tara dake karkashin dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afrika wato FOCAC, da sakamakon taron ministoci karo na 8 na dandalin, sun dace matuka da agandar da AU ke son cimmawa zuwa 2063, haka kuma, za su inganta hadin gwiwar Sin da Afrika a fannin samar da ci gaba a dukkan bangarori.

Jami’ar ta bayyana haka ne yayin da take zantawa da manema labarai a baya-bayan nan, a hedkwatar AU dake birnin Addis Abbaba na Habasha.

Ta kuma kara da cewa, ayyukan tara, na mayar da hankali ne kacokan kan moriyar jama’a, kuma AU na sa ran ganin hakan. (Fa’iza Mustapha)