logo

HAUSA

MDD za ta taimakawa kasashen Afirka wajen raya sashen hada hadar basussuka

2022-08-24 13:45:23 CMG HAUSA

 

Shugaban sashen lura da kasuwannin hada-hadar basussuka, bangaren raya harkokin sassa masu zaman kansu, a hukumar UNECA ta MDD Sonia Essobmadje, ya ce MDDr na shirin samar da tsari da zai taimakawa kasashen nahiyar Afirka, wajen raya sashen hada-hadar basussuka na cikin gida, domin ingiza bunkasar tattalin arzikinsu.

Sonia Essobmadje, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua hakan ne a birnin Nairobin kasar Kenya. Yana mai cewa, nahiyar Afirka na fama da rashin ci gaba, a fannin hada-hadar basussuka masu dogon zango na cikin gida, wanda hakan ke takawa sassa masu zaman kansu, da manyan ayyukan more rayuwar jama’a birki.

Jami’in wanda ya yi tsokacin, a gefen taron nazari game da dabarun bunkasa hada hadar kasuwannin basussuka a Afrika da ya gudana a jiya Talata, ya ce idan aka inganta sashen, zai bude wata dama ga kamfanonin waje, ta zuba karin jari a kasashen nahiyar.

Essobmadje ya kara da cewa, idan kasashen Afirka suka samu wannan dama, za su rage dogaro ga basussuka daga kasashen ketare, domin gudanar da ayyukan raya kasa. Ya ce ingantattun kasuwannin samar da basussuka na cikin gida, na taka muhimmiyar rawa wajen samar da basussuka na cikin gida da na ketare, tare da baiwa gwamnatoci damar cike gibin kasafin kudi da suke tsarawa.   (Saminu Alhassan)