logo

HAUSA

Yakin Afghanistan ba fim ba ne

2022-08-24 17:17:46 CMG Hausa

“Dana daya ya fado daga jirgin sama a filin jiragen sama na Kabul, dayan kuma har yanzu ba mu san inda yake ba”. Kalaman da Mohammad Rezayee, dan kasar Afghanistan ya yi a kwanan baya a yayin da yake tattaunawa tare da jaridar The Times ta Burtaniya a kwanan baya, sun tunatar da mu kan abin da ya faru a shekara daya da ta gabata. A watan Agustan shekarar 2021, Amurka ta janye sojojinta daga kasar Afghanistan ba tare da daukar nauyin da ke bisa wuyanta ba, matakin da ya sa dubu dubantar ‘yan Afghanistan suka kutsa cikin filin jiragen sama na Kabul, inda jiragen saman dakon kaya na sojan Amurka suka tashi ba tare da yin la’akari da yadda ‘yan Afghanistan ke kokarin neman shiga jiragen, matakin da ya sa mutane da dama suka fado daga jirgin, kuma Zabi Rezayee mai shekaru 17 da haihuwa kuma dan Mohammad Rezayee, na daya daga cikin wadanda suka fado, a yayin da Zaki Rezayee, dansa na daban wanda a lokacin shi ma ya ke kan jirgin, amma an rasa inda yake.

Yanzu iyalan Mohammad Rezayee na fuskantar kuncin rayuwa, sun sayar da kadarorinsu, kuma ba yadda za su yi su rufe shagon sai da ‘ya’yan itatuwa da ganyayen lambu da suka gudanar, duk da haka, wani lokaci ba su iya biya kudin burodi ba.

Abin da ya faru ga Mohammad Rezayee, yana kuma faruwa ga sauran ‘yan kasar ta Afghanistan. Duk da cewa, a karshen watan Agustan bara, Amurka ta dasa aya ga yakin Afghanistan da ya tayar bisa sunan “yaki da ta’addanci”, amma ga mawuyacin halin da yakin ya haifar ga al’ummar kasar. Baya ga haka, duk da cewa Amurka din ta janye sojojinta, amma tana ci gaba da kakaba wa kasar takunkumi, har ma ta haramta al’ummar kasar da ke fama da kunci yin amfani da kudadensu tare da neman satar wani kasonsu, lamarin da ya haifar da matsalar jin kai mai tsanani a kasar. David Howell Petraeus, tsohon shugaban hukumar leken asiri ta kasar Amurka, ya taba amincewa da laifin da Amurka ta aikata cikin shekaru 20 da suka wuce a yayin da ta tura sojojin zuwa Afghanistan, kuma a yayin da ya tabo magana a kan yakin Afghanistan, ya kan ce, “ya yiwu ka gaji da kallon wani fim, kuma ka bar gidan sinima, a yayin da kuma fim din na ci gaba”.

Sai dai yakin Afghanistan ba fim ba ne. Yakin da Amurka ta kaddamar a Afghanistan cikin shekaru 20 da suka wuce, ya lalata kasar da kuma makomar al’ummar kasar, tare da halaka mutane dubu 174, ciki har da fararen hula sama da dubu 30, baya ga kuma miliyoyin al’ummar kasar suka zama ‘yan gudun hijira. Lallai Amurka ta tafi bayan da ta gaji da yakin, amma da wuya a kawar da raunin da ya haifar ga al’ummar Afghanistan, wadanda yanzu haka miliyan 18.0 ke matukar fama da matsalar karancin abinci, kuma yara miliyan 3 sun kasa samun damar shiga makaranta.

Nan da wasu kwanaki, za a cika shekara guda da Amurka ta janye sojojinta daga Afghanistan. Ya kamata gwamnatin Amurka ta yi na’am da laifukan da ta aikata, kuma ta dauki matakan da suka wajaba don biyan hasarorin da al’ummar Afghanistan suka sha. Wani abu da ya fi muhimmanci kuma shi ne, bai kamata a manta da yakin Afghanistan ba, musamman ma kasar Amurka, dole ta koyi darasi daga yakin. (Mai zane:Mustapha Bulama)