logo

HAUSA

Cibiyoyin hada-hadar kudi na kasashen Najeriya da Faransa sun rattaba hannu kan yarjejeniyar bayar da lamuni ta Euro miliyan 100 don magance matsalar sauyin yanayi

2022-08-24 13:58:36 CMG Hausa

Bankin masana'antu a Najeriya, ya rattaba hannu kan wata yarjejeniyar lamunin Euro miliyan 100, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 99.5 da hukumar raya kasar Faransa (AFD), don samar da kudaden gudanar da ayyukan magance matsalar sauyin yanayi.

Manajan daraktan bankin, Olukayode Pitan ne ya bayyana haka a yayin bikin rattaba hannun da ya gudana jiya Talata, yana mai cewa, rancen na tsawon shekaru 10, na da kudin ruwa na kaso 2.47 a duk shekara, da jinkirin fara biya na tsawon shekaru hudu.

Pitan ya ce, rancen zai mayar da hankali ne musamman kan ayyuka da suka shafi makamashin da ake sabuntawa, da rage fitar da iskar carbon, da samar da isasshen makamashi, da fasahar noma mai jure yanayi, da tsaftataccen sufurin birane, da sauransu.

Daraktan AFD a Najeriya Xavier Muron, ya bayyana a yayin bikin cewa, wannan sabon tsari na bashi, wani mataki ne na cimma nasarar yarjejeniyar sauyin yanayi ta Paris, kuma ya zo a dai-dai lokacin da Najeriya ke fatan kaddamar da sabon shirinta na samar da wutar lantarki.(Ibrahim)