logo

HAUSA

Sin Da Afirka Na Samun Ci Gaban Hadin Gwiwa: Waiwaye Ga Jawabin Wang Yi

2022-08-24 10:01:23 CMG Hausa

Har kullum mahukuntan kasar Sin na jaddada muhimmancin hada gwiwa da kasashe masu tasowa, musamman ma na nahiyar Afirka, wadanda Sin din ke dauka a matsayin abokan hulda kuma aminai da take yin kawance na hakika da su. 

Kasar Sin na daukar kasashen Afirka a matsayin abokan cimma nasara ta zahiri. Karkashin manufofin karfafa abota, da goyon bayan juna, da hadin gwiwa, sassan biyu na fatan cimma sabbin nasarori na bai daya a sabon zamani da ake ciki.

Cikin jawabin da ya gabatar kwanan baya, yayin taro manyan wakilai, game da nazarin matakan aiwatar da manufofin taron ministocin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka ko FOCAC karo na 8, dan majalissar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya tabo batu kan taron ministocin FOCAC da ya gudana a birnin Dakar na kasar Senegal a watan Nuwambar 2021, wanda ya aza wani ginshiki mai karfi, game da karfafa alakar Sin da kasashen nahiyar Afirka. Tare da waiwaye kan burin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ke da shi, na yin aiki tare da kasashen Afirka, wajen aiwatar da muhimman ayyuka 9, matakin da ya yi matukar samun karbuwa ga kasashen nahiyar, a matsayin ginshikin bunkasa ci gaban Afirka, tare da daga maysayin hadingwiwar sassan 2. (Saminu Hassan, Ibrahim Yaya, Sanusi Chen)

Idan an waiwayi baya, za mu ga yadda sassan biyu, wato Sin da kasashen Afirka suka yi aiki tare, wajen shawo kan wahalhalu da kalubale daban daban, ciki har da yaki da annobar COVID-19, suka kuma yi aiki kafada da kafada, wajen aiwatar da sakamakon taro na 8, na ministocin kasashen dandalin FOCAC. Sin ta kuma tallafawa wasu kasashen nahiyar da hatsi, domin dakike kamfar abinci, da fari da suka sha fama da su. Ta amince da yin tafiya tare da su a fannin bunkasa ci gaba mai dorewa, da ingiza zaman lafiya da aidaito. Don haka dai ana iya cewa, hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka, na taka muhimmiyar rawa a fannin gina al’ummar Sin da Afirka mai makomar bai daya a sabon zamani. 


A halin yanzu kuma, Sin na fatan zurfafa amincewa da juna, da nunawa juna goyon baya tsakaninta da aminanta na Afirka, da ingiza ci gaban bai daya, da tallafawa fannin shawo kan kamfar abinci a Afirka, ta hanyar samar da tallafi, da shigar da sabbin fasahohin inganta noma, da taimakawa fannin wanzar da tsaro, da karfafa kawance tsakanin al’ummun sassan biyu.