logo

HAUSA

Sin da kasashen Afirka na ci gaba da habaka hadin gwiwa a fannin aikin noma

2022-08-24 15:15:02 CMG HAUSA

 

Kasar Sin ta dade tana mai da hankali kan yadda kasashen duniya baki daya za su iya samun ci gaban tare, ta yadda kowane yanki na duniyarmu zai iya samun kyakkyawar makoma. A fannin aikin noma, Sin ta raba kwarewarta, da fasahohinta ga kasashen Afirka, da habaka sassan cin gajiyar albarkatun noma da bunkasa cinikin kayayyakin amfanin gona, da kuma neman samun hanyoyin zamani na sabunta harkar noma, ta yadda karkashin hakan, al’ummar kasashen Afirka za su iya samun isasshen hatsi da karin kudaden shiga. Kaza lika Sin, ta ba da gudummawa ga cimma makasudin kawar da yunwa da talauci daga nahiyar Afirka.

Shugabar shirin aikin noma da samar da abinci na MDD Maria Helena Semedo, ta bayyana cewa, kasar Sin ta samar da misalai da ayyuka masu kyau da yawa a fannin aikin gona, game da yadda aka hada da cin gajiyar albarkatun kasa, da binciken kimiyya, wadanda suka tabbatar da samar da isassun kayayyakin abinci, da abinci mai gina jiki, da kuma tabbatar da rayuwar jama’a ta yau da kullum, tare da kula da ci gaba mai dorewa a fannin kare muhalli.(Safiyah Ma)