logo

HAUSA

Ya kamata Birtaniya ta girmama alkawarin da ta dauka game da batun tsibiran Malvinas

2022-08-23 11:01:03 CMG HAUSA

Kwanan baya, ofishin jakadancin Birtaniya dake Argentina, ya gabatar da wata gasar bidiyo a kan yanar gizo, ga daliban jami’o’in dake kasar, inda ofishin ya yi ikirarin cewa, wanda ya lashe gasar zai samu damar yin ziyarar mako guda kyauta a tsibiran Malvinas.

Game da hakan, ma’aikatar harkokin wajen kasar Argentina, ta fitar da sanarwar nuna rashin jin dadin ta, inda ta ce, matakin da Birtaniya ta dauka na nufin cewa tana mallakar tsibiran, don haka ta bukaci Birtaniya da ta cika alkawarin da ta dauka karkashin kudurin MDD, kana ta yi shawarwari da Argentina game da ikon mulkin tsibiran.

A shekarar 1816, Argentina ta samu ‘yanci daga mulkin mallakar kasar Spaniya, tare da samun ikon mulkin tsibiran Malvinas, amma lokacin da Birtaniya ta habaka mulkin mallakarta a kudancin nahiyar Amurka, ta mamaye tsibiran na Malvinas a shekarar 1833. A shekarar 1982, yakin da aka gwabza na tsawon kwanaki 74 tsakanin kasashen biyu, domin karbe ikon mulkin tsibiran, ya kai ga Birtaniya ta samun nasara. Amma duk da haka, Argentina ba ta taba yi watsi da ikon mulkin tsibiran ba. Kwamitin hana mulkin mallaka na MDD, ya fitar da kuduri har fiye da sau 30, don kalubalantar gwamnatin Birtaniya, da Argentina, da su yi shawarwari kan batun, kuma sau da dama Argentina ta gaggayci Birtaniya da ta shiga shawarwari, amma Birtaniya ta ki karbar gayyatar.

Birtaniya ba za ta canja ikon mulkin tsibiran ba, saboda shaiddu da ake da su game da batun, duk da atisayen soja, ko na makamai da take girkewa, ko gasar da za ta gudanar da sauransu ba.

A watan Maris na shekarar 2016, kwamitin tabbatar da iyakokin bangarorin duniya na MDD, ya ba da tabbacin cewa, Argentina na da ikon mulkin tsibiran Malvinas. Ban da wannan kuma, kimanin dukkan kasashe dake nahiyar Latin Amurka, da yankin Caribbean, suna goyon bayan Argentina game da batun. Kaza lika ita ma kasar Sin tana marawa Argentina baya, kan ikon mulkin tsibiran. (Amina Xu)