logo

HAUSA

Pingcuo Wangzha matashi ne da ke kokarin zama likita

2022-08-23 08:15:42 CMG Hausa

Kwanan baya, Pingcuo Wangzha, wani matashi dan jihar Tibet ta kasar Sin, ya samu damar shiga shahararriyar jami’ar Beijing, bayan ya ci jarrabawar shiga jami’a. Zai shafe shekaru 8 yana koyon ilmin likitanci, don zama wani likita a nan gaba.

Pingcuo ya fito ne daga wani iyalin likitoci. Kakanninsa, da mahaifinsa dukkansu likitoci ne, kana yayansa yana neman samun digiri na biyu a fannin ilmin likitanci. Pingcuo ya yi fatan cewa, zai koma garinsa Tibet bayan ya zama likita don taimakawa ‘yan garin da fasahar kiwon lafiya ta zamani. (Tasallah Yuan)