logo

HAUSA

Jamilu Garba Usman: Zan kara kokari don tallata yaren Sinanci a Najeriya

2022-08-23 14:55:12 CMG Hausa

Jamilu Garba Usman, malami ne dake koyar da yaren Sinanci a halin yanzu, a makarantar koyar da yaren Sin dake garin Kwankwaso na jihar Kano a arewacin Najeriya, wato Chinese Bilingual College.

A zantawarsa da Murtala Zhang, malam Jamilu, wanda ya taba koyon yaren Sinanci a birnin Changsha na lardin Hunan a wasu shekarun da suka gabata, ya bayyana yanayin makarantar, da muhimmancin koyon wannan yare. Sa’annan ya bayyana cewa, ta hanyar karatun yaren Sinanci, ya kara fahimtar al’adu da halayen mutanen China.

A karshe, malam Jamilu ya ba da shawara ga al’ummun Najeriya da suke sha’awar koyon yaren Sinanci. (Murtala Zhang)