logo

HAUSA

Gyambon gindin hakora ya raunana kwarewar fahimta ta masu fama da ciwon Alzheimer's disease a farkon lokacin fama da ciwon

2022-08-23 11:32:47 CMG Hausa

Masu nazari daga kasar Birtaniya sun kaddamar da rahotonsu a kwanakin baya cewa, gyambon kasan hakora na haifar da saurin lalacewar kwarewar fahimta ta masu fama da cutar karancin basira ko kuma Alzheimer's disease a bakin Turawa a farkon lokacin fama da ciwon.

Mene ne ma’anar cutar Alzheimer's? Alzheimer's wani nau’in cut ace ta karancin basira da ya fi damun mutane, wanda ke farawa daga matsalar mantuwa, da gazawa wajen yin magana, daga bisani ya shafi tunanin mutane da kwarewar magana har ma da gudanar da harkokin yau da kullum. Abin bakin ciki shi ne ya zuwa yanzu dai babu wata kyakkyawar hanyar shawo kan cutar, kuma babu wani nau’in magani da zai kare mu daga kamuwa da ita.

Masu nazari daga jami’ar Southampton da kuma kwalejin sarki na jami’ar London na kasar Birtaniya sun dauki watanni 6 suna bibbiyar mutane 59 masu fama da cutar karancin basira ta Alzheimer's kadan da matsakaici, dangane da kwarewarsu ta fahimta da bakinsu, tare diba da nazarin jininsu a tsanake.

Masu nazarin sun gano cewa, idan wadannan masu fama da cutar suka  kamu da gyambon kewayen hakora, to, a cikin watannin 6 ne lalacewar kwarewarsu ta fahimta ta fi ta sauran mutane sauri har sau 6, kana kuma sun fi saukin samun kumburi a jikunansu.

Dangane da lamarin, masu nazarin sun yi karin bayani da cewa, watakila dalilin da ya sa haka shi ne, domin gyambon kewayen hakora ya yi illa ga kwarewar fahimtar masu fama da cutar karancin basira ta Alzheimer's, karkashin tsarin jikin dan Adam na daidaita kumbura a jiki.

Madam Zhang Chuji, likita ce da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta ba mu shawarar cewa, idan masu fama da cutar karancin basira ta Alzheimer's suka kamu da gyambon kewayen hakora, to, zai fi kyau su je ganin likita cikin hanzari, saboda watakila hakan zai rage saurin bullowar alamun cutar karancin basira ta Alzheimer's. (Tasallah Yuan)