logo

HAUSA

Ranar Chushu

2022-08-23 17:05:48 CMG Hausa

Yau rana ce ta Chushu, bisa tsarin alamu 24 na sauyawar yanayi cikin shekara, wanda tun kaka da kakanin Sinawa suka kirkiro. Ma’anar Chushu shi ne karshen zafi, wato daga yanzu lokacin zafi ya kare ke nan, kuma an shiga yanayin kaka. Don haka, ranar na da muhimmanci sosai ga manoma, kasancewar daga ranar, manoman za su fara girbin amfanin gonarsu.(Lubabatu)