logo

HAUSA

An kusa kammala katafaren aikin samar da wuta lantarki na gabashin Afirka

2022-08-22 14:50:51 CMG Hausa

Sashen dake kula da shirin babban aikin samar da wutar lantarki a madadin gwamnatocin kasashen Burundi da Rwanda da Tanzaniya, (NELSAP-CU) ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, aikin samar da wutar lantarkin na yankin magangar ruwan Rusumo Falls, ya kai kashi 95 cikin 100 na fara aiki.

Idan aikin ya samar da wutar lantarki mai karfin megawatt 80 na yankin Rusumo Falls dake kan iyakar Rusumo tsakanin Rwanda da Tanzaniya ya kammala, ana saran zai amfanar da sama da mutane miliyan daya a yankin gabashin Afirka.

Ministan ababen more rayuwa na kasar Rwanda Ernest Nsabimana, wanda ya jagoranci majalisar ministocin dake kula da aikin a ranar Asabar don duba ci gaba aikin., ya bayyana cewa, idan aikin ya kammala, zai bunkasa harkokin tattalin arziki, da kamfanoni masu zaman kansu, da zuba jari kan ababen more rayuwa ta hanyar inganta samar da wutar lantarki a yankin.(Ibrahim)