logo

HAUSA

MDD ta bukaci tallafin dogon lokaci ga wadanda abin ya shafa a Somaliya sakamakon karuwar hare-hare

2022-08-22 11:14:02 CMG Hausa

 

Babban wakilin MDD a kasar Somaliya James Swan, ya yi kira da a samar da tallafi mai dorewa ga wadanda lamarin ya shafa a Somaliya, a daidai gabar da ake fama da hare-haren 'yan ta'addar al-Shabab a fadin kasar.

James Swan ya bukaci a gaggauta baiwa wadanda lamarin ya shafa da iyalansu tallafi kuma na dogon lokaci.

Ya ce, wajibi ne a saurari koke-koken wadanda suka tsira da rayukansu, a kuma bi masu hakkinsu. Yana mai cewa, ta'addancin da aka aikata a birnin Mogadishu a karshen mako, wani babban abin tunatarwa ne, duba da muhimmancin hakan.

Bayanin na wakilin MDD na ya zo ne, bayan da jami'an tsaron Somaliya suka kawo karshen kawanyan sa'o'i 30 da mayakan al-Shabab suka yi wa otel din Hayat.

Wani jami’in ‘yan sanda ya bayyana cewa, jami’an tsaro na musamman, sun kashe maharan da suka tayar da bama-baman, inda suka kutsa kai cikin fitaccen otel din, da galibi fararen hula, da jami’an gwamnati, da ‘yan majalisa suke fi zuwa.

Sai dai mazauna garin sun ce, sun ji karar harbe-harbe a cikin otal din jiya da safe.

Ministan lafiya na kasar Somaliya ya sanar a jiya cewa, mutane 21 ne suka mutu yayin da wasu 117 kuma suka jikkata a harin da aka kai a otel din dake Mogadishu,babban birnin kasar. (Ibrahim)