logo

HAUSA

Yang Ning: Sadaukar da kanta wajen horar da matasa don raya mahaifarsu

2022-08-22 14:52:29 CMG Hausa

Yang Ning ta kasance yar asalin Jiangmen, wani kauye dake jihar Guangxi ta kabilar Zhuang mai cin gashin kanta a kudancin kasar Sin. A shekarar 2010, bayan ta kammala jamia a Nanning, babban birnin jihar Guangxi, inda ta karanta fannin tafiyar da harkokin kasuwanci, ta koma Jiangmen domin aiki a matsayin jamiar kauye. A yanzu, Yang Ning ce daraktan kwamitin kauyen. Ta kuma sadaukar da kanta wajen raya mahaifarta tare da taimakawa wajen horar da matasan kauyen.  

Yang Ning ta bayyana cewa, na bar gida domin karatu ne a lokacin da nake shekaru 12, kuma na dawo gida bayan na kammala jamia. Idan aka kwatanta da yankunan waje, rayuwa a garinmu ya fi sauki da kuma ganin ainihin rayuwa. Na fi kowa fahimtar cewa, kauyenmu na bukatar matasan da za su jagorance shi wajen samun kyautatuwar rayuwa.

Akwai kusan iyalai 500 a kauyen Jiangmen. Mazaunansa sun shafe gomman shekaru suna zaune cikin talauci. A shekarar 2010, ko wanne mutumin kauyen na samun kimanin yuan 100, kwatankwacin dala 153 ne a shekara.

“Na ga yadda wasu birane ke samun ci gaba cikin sauri. Bayan na dawo garinmu, ban ji dadin ganin talauci da koma bayan da ake fama da su ba. A wannan lokaci, na yanke shawarar sauya yanayin da taimakawa mazauna fatattakar talauci da kyautata rayuwarsu, cewar Yang.

Nan da nan Yang ta fahimci cewa, aiki a kauyen ya bambanta da abun da ta yi tunani. A wani lokaci, akwai abubuwan yi da yawa, da ba ta san ta inda za ta fara ba. Ta kuma gane cewa, babu wata gajeriyar hanya da za ta bi, don haka dole ne ta yi hakuri ta ci gaba da nazari da koyo ta hanyar gwada abubuwa.

Wata rana, Yang ta taimakawa wani dattijon da bai iya karatu ba cike fom, domin ya nemi kudin gudanar da harkokin yau da kullum da gwamnatin kasar Sin ke bayarwa. A washegari da ta isa ofis, bayan ta gama aiki a kauyen, sai Yang ta ga wani dattijo zaune a gaban ofishinta. Ya ba Yang lemu, domin gode mata bisa taimaka masa da ta yi wajen cike fom din. Yang ta ce, wani dan abu kadan na yi masa, amma ya taimaka masa sosai da iyalinsa. Ya sa na ji cewa, aikina yana da maana. Mutanen kauyen na da kirki, kuma ina son taimaka musu.

Yang ta yi iyakar kokarin taimakawa mutanen kauyen shawo kan matsalolinsu. Pan Jianqiang, wani dattijo ne da yake kwance saboda rashin lafiya. Yang kan kai masa magani akai-akai, kana ta taimaka masa samun tallafin kudi daga gidauniyar Tencent.

A wani lokaci ma, Yang ta taba taimakawa wata yarinya da iyayenta matalauta ne, na tsawon shekaru 6 domin ta samu damar kammala karatu. Yanzu yarinyar da iyayenta na zama a gunduma, kuma rayuwarsu na ci gaba da kyautatuwa.

Domin taimakawa karin yara a kauyen, Yang ta kafa wani gida ga yaran da iyayensu suke aiki a birane. Tana amfani da lokacinta wajen wasanni da yaran. A shekarar 2013, Yang ta shirya wani yawon shakatawa a lokacin rani, inda ta gayyaci daliban jamia su raka yaran. Yang ta kan gudanar da ayyukanta bisa tsari, cewar Jia Lixian, mataimakiyar darakta a kwamitin kauyen, kuma shugabar kungiyar mata ta Jiangmen.

Lalubo hanyar fitar da mutane daga kangin talauci, daya ne daga cikin manyan burikan Yang. Ya kamata mu yi cikakken amfani da albarkatun dake akwai a Jiangmen, kuma mu raya muhallin shuke-shuke, cewar Yang.

Bisa laakari da dimbin albarkatun gora da wurin ke da shi, Jiangmen na wani wurin da ya dace da raya aikin sarrafa gora. A 2021, bayan gudanar da nazarin kasuwa, Yang ta gamsu cewa sayar da kayayyakin gora da aka sarrafa kai tsaye ga masu saye a lardunan Guangdong da Guangxi, zai taimakawa mutanen kauyen samun karin kudin shiga. Don haka, ta tuntubi masu saye, ta kuma taimakawa mutanen rattaba hannu kan yarjejeniyoyi da musu sayen. A sakamakon haka, manoman gora da masu sarrafa shi a kauyen, sun samu karin kudin shiga.  

A 2014, mutanen kauyen da dama suka fara noman tattasai, amma mamakon ruwan sama da aka yi a shekarar, ya sa tattasan rubewa. A shekara mai zuwa kuma, Yang ta jagoranci iyalai 90 wajen shuka saiwar Kudzuvine. Yang ta waiwaya cewa, ba abu ne mai sauki jagorantar mutanen kauyen samun saa da yaki da fatara ba.

Ta kuma karfafawa mutanen rungumar dabarun noma na gargajiya na kabilar Miao, domin noman shinkafa a muhalli mai dacewa da kuma daina amfani da maganin kashe kwari da takin zamani. Wasu sun yi shakkun samun amfanin gona idan suka yi amfani da dabarun gargajiya. Amma domin kawar da shakkun, sai Yang da sauran wasu mutanen kauyen suka jagoranci noma na gwaji. A kuma lokacin kaka, sun samu girbi mai armashi, kana sun sayar da shinkafan kan farashi mai rahusa. Daga nan, karin mutane suka bi dabarun Yang na noman shinkafa da kayan marmari da na lambu.

Haka kuma, Yang ta kaddamar da wani shirin karawa juna sani na yaki da talauci, ta hanyar sarrafa amfanin gona a kauyen, kuma kayayyakin na samun kasuwa sosai.

Irin rikon gaskiya na Yang, ya sa mazauna kauyen suka aminta da ita. Yang Meiyang, wata kurma, ta bayyana ta hanyar magana da hannu cewa, “a shirye nake in yi duk abun da Yang ta ce in yi.(Kande Gao)