logo

HAUSA

Nasarorin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka A Shekaru Goman Baya

2022-08-22 16:04:47 CMG Hausa

Hulda dai tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka ta fara ne da dadewa tun a lokacin da kasar Sin tana hada hadar cinikayya da kasashen ketare a kan dadaddiyyar “hanyar siliki’’ da kuma lokacin gwagwarmayar neman ’yanci da Afirka ta yi fama da shi daga hannun ’yan mulkin mallaka daga farkon 1950 wanda kasar Sin ta yi rawar gani domin ganin kasashen Afirka sun samu ’yancin kai.

A sakamakon samun ’yancin da ci gaba da kulla huldar diplomasiyya ne kasashen na Sin da Afirka suka samu damar kulla zumunta wadda ta kai ga irin hadin gwiwar da ake da shi a yau, inda har sassan biyu suka kafa dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka wato FOCAC a shekarar 2000, wanda cikin shekaru sama da 20 da suka wuce, ya haifar da gaggaruman nasarori masu tarin yawa ga hadin gwiwar sassan biyu, tare da amfanawa al’ummunsu.

A ci gaba da wannan dangantaka ne kasashen Afirka da dama suka shiga shawarar da  shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kirkiro a shekarar 2013, wadda aka fi sani da BRI wato “ziri daya da hanya daya’’. Wannan shawara ta BRI ta samu karbuwa a yayin da kasashen Afirka sama da 50 suka rattaba hannu domin hadin gwiwar aiwatar da ita, shawarar tana kunshe da alfanu da tasiri da kuma tabbacin ci gaba na kasashe mambobi.

A karkasin shirin BRI wato “ziri daya da hanya daya”, a yanzu haka nasarorinsa sun bayyana kuma sun zama zahiri a idanun kowa. Makasudin wannan hadin gwiwar ta hanyar samar da tallafi ma kasashe masu tasowa dake da gibin kudaden gina ababen more rayuwa kamar hanyar jirgin kasa wato layin dogo da filayen jiragen sama da hanyoyin mota da tashoshin jiragen ruwa da dam-dam don samun wutar lantarki da ruwan sha da dai sauransu.

A sani na ne, kuma ni ganau ne ga nasarorin da irin hadin gwiwar Sin da Afirka suka cimma, har ma a ce a kasata Najeriya a shekaru goman da suka wuce. A Najeriya dai hadin gwiwar ya haifar da gagaruman ci gaba ta fannoni da dama a kasar, kamar layin dogo daga Abuja zuwa Kaduna da layin dogo na Lagos zuwa Ibadan da layin dogo mai zirga-zirga a cikin garin Abuja zuwa filin jirgin sama. Haka zalika a karkashin wannan hadin gwiwar an samu kammala kayatar da filayen jiragen sama na zamani a manyan biranen Abuja da Lagos da Fatakwal da Kano. Akwai hanyoyin mota kamar hanyar Abuja zuwa Lafiya da kuma Kano zuwa Katsina wadanda yanzu haka aikinsu ya yi nisa.

Ba da jimawa da kaddamar da layin dogo na Abuja zuwa Kaduna ne na shiga wannan jirgin kasa zuwa Kaduna, lallai akwai kayatarwa domin wannan layin dogo shi ne na farko da ya hada Abuja da Kaduna. Tafiyar dai ta bambamta da amfani da mota domin kuma akwai sauki. Hakazalika, akwai layin dogo mai zirga zirga a cikin Abuja wanda shi ma na dana shi zuwa filin jigin sama na Abuja. Wannan layin dogon cikin gari akasari yana sufurin fasinjoji ne daga cikin garin Abuja zuwa tashar filin jirgin sama ta Abuja domin saukaka wa matafiya. Haka kuma ita ma sabuwar tashar jiragen sama da aka gina karkashin wannan hadin gwiwar na yi amfani da ita kuma tsarinta, da girmanta ya gamsu domin kuwa komai na zamani ne a cikinta kuma za ta ja da duk wata tashar jiragen sama a duniya.

Kasashe dai fiye da 35 a yanzu haka suke cin amfanin irin wannan hadin gwiwar kuma kwalliya na biyan kudin sabulu a duk inda aka fara gina wani abu, ko dasa wani abu a tsawon shekaru goma da suka wuce. A kasar Habasha ma an samu babbar nasara a yayin da aka kammala layin dogo daga Addis Ababa zuwa tashar jirgin ruwa to Djibouti a farkon shekarar 2018. A kasar Kenya ma an yi nasarar kammala layin dogo daga babban birnin Nairobi zuwa tashar jirgin ruwa to Mombasa a shekarar 2017. A Ghana ma an iyar gina Bui dam a shekarar 2013 wanda shi ne gagarumin aikin da hadin gwiwar Sin da kasar ta Ghana ta samu domin jin dadin jama’ar kasar.

Fahimta ta a kan wadannan nasarori a karkashin hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka ta nuna cewa kawance da dankon zumunci wadanda yana kamari tsakanin Sin da kasashen na Afirka kuma kasar Sin ta nuna cewa kasa ce da za’a iya dogaro da ita a kowane lokaci kuma cikin kowane irin halin da kawayenta na Afirka suka samu kansu a ciki, kuma ba da wasu sharuddan kaskantarwa ba ko tsoma baki a harkokin siyasa da na cikin gidan kowace kasa ba. Fatarmu shi ne wannan dangantaka da aminci su dore domin kyautata zamantakewa tsakanin jama’ar mu baki daya. (Lawal Sale)