logo

HAUSA

Amurka Mai Satar Mai Daga Kasar Sham

2022-08-22 14:07:53 CMG HAUSA

DAGA MINA

Abokai, kwanan baya an bankado wasu ayarin motocin dakon mai na sojin Amurka sunafitar da man da suka sata daga kasar Sham zuwa sansaninsu dake Iraqi ta wata hanya da ta hada kasar Sham da Iraqi.Tun daga shekarar 2015, Amurka ta fara aikata irin wannan laifi,awatan Agustan da muke ciki kadai,Amurka ta aikata irin wannan abin kunya na satar mai da fitar da shi zuwa Iraqi har a kalla sau 6.Yayin da fararen hula a birnin Damascus babban birnin kasar, ke dogoyen layi don sayen man. “Duniya a zanen MINA” na zana wani hoto game da yadda Amurka ta saci mai a kasar Sham.

Hukumar man fetur da albarkatun ma’addinai ta kasar Sham ta ba da sanarwa a kwanan baya cewa, a watanni shida na farkon wannan shekara, a ko wace rana ana samar da man da ya kai ganguna dubu 80.3 a kasar, amma Amurka da dakarunta sun sace kaso 80% daga cikinsu. Rahotanni na cewa, kasar Sham ta yi asarar kudaden da suka kai kimanin dalar Amurka biliyan 100 sakamakon satar mai da Amurka ta yi. Amma, Amurka ta nuna ko-in-kula game da sanarwar da kasar ta sha bayarwa. Saboda muhimmancin man fetur din, tana yunkuri kwace shi, ba tare da yin la’akari da halin da al’ummar kasar Sham ke ciki ba ko kadan.

Da ma yake-yake na addabar al’ummar Sham, ga shi kuma satar man da Amurka ta yi ya yi sanadin gurgunta tattalin arziki da haifar da hauhawar farashin mai a kasar, abin da ya jefa al’ummar kasar cikin hali mai wuya.  Amurka, tana farin ciki ne da samun mai ba tare da biya ba, sai dai wa zai kwantar da hankalin jama’ar kasar? (Mai zane: MINA)