logo

HAUSA

Mutane 21 sun mutu sanadiyyar harin otel na Mogadishu

2022-08-21 19:47:59 CMG Hausa

Ma’aikatar lafiya ta kasar Somalia ta sanar a yau Lahadi cewa, mutane 21 sun mutu yayin da wasu 117 suka jikkata, a harin da aka kai wa otel din dake Mogadishu, babban birnin kasar.

Da farko, kwamadan ‘yan sandan Mogadishu Abdi Hajar, ya sanar da kawo karshen kawanyar da mayakan Al-Shabab suka yi wa otel din na Hayat dake birnin Mogadishu, yana mai cewa, an ceto mutane 106. (Fa’iza Mustapha)