logo

HAUSA

Masanin Najeriya: Sin aminiyar kasashen Afirka ce a ko da yaushe

2022-08-21 16:02:02 CMG Hausa

An kira taron masu shiga tsakani na tabbatar da sakamakon taron ministoci karo na 8 na dandalin taron tattauna hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka a ranar 18 ga wannan wata ta kafar bidiyo, inda shehun malami a cibiyar nazarin yadda ake daidaita rikici da wanzar da zaman lafiya ta tarayyar Najeriya, Oboshi Agyeno ya bayyana yayin da yake zantawa da wakilinmu na CMG cewa, sakamakon da aka cimma a jere yayin taron sun nuna cewa, a ko da yaushe kasar Sin ta kasance babbar aminiya ga kasashen Afirka.

Oboshi Agyeno ya kara da cewa, kasar Sin ta dade tana nacewa kan manufar “kasashen Afirka su daidaita matsala ta hanyar da ta dace da su”, kuma har kullum tana taimakawa kasashen Afirka yayin da suke tsara hanyar daidaita matsalar, abubuwan da suka shaida cewa, kasar Sin aminiyar kasashen Afirka ce a ko da yaushe.

Oboshi Agyeno ya kara da cewa, ya dace masu tsara manufofi da ‘yan siyasa da sauran masana masu ruwa da tsaki, su yi kokari domin ingiza huldar dake tsakanin Sin da Afirka ta hanyar kirkire kirkire, ta yadda za a gina kyakkyawar makomar Sin da Afirka a sabon zamanin da ake ciki, tare kuma da ciyar da tattalin arziki da zamantakewar al’ummar Afrika gaba, da kyautata rayuwar al’ummomin Afirka yadda ya kamata. (Jamila)