logo

HAUSA

Gwamnatin Nijeriya ta matse kaimi wajen yaki da kungiyoyin ‘yan ta’adda a kasar

2022-08-21 15:42:45 CMG Hausa

Rundunonin tsaro a Nijeriya sun matse kaimi wajen yaki da kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi da sauran ‘yan ta’adda, domin magance kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta

Ministan kula da tsaron Nijeriya Bashir Magashi ne ya bayyana haka a jiya, inda ya ce rundunar soji da sauran hukumomin tsaro, sun hada gwiwa domin zakulo ‘yan ta’adda daga maboyarsu.

Ya ce an tura jami’an tsaro manyan titunan da suke fuskantar barazanar hare-hare, da yankunan arewa maso tsakiya da arewa maso yammacin kasar, domin farautar ‘yan ta’addan dake boye a dazuka, yana mai cewa, kawo yanzu, jami’an sun lalata sansanonin bata garin da dama tare da ceto mutanen da suka sace.

A cewarsa, cikin watannin baya-bayan nan, ‘yan ta’adda 70,000 da iyalansu, sun mika wuya ga jami’an tsaro, inda kuma dubban mutanen da suka tsere, suka koma gidajensu.

Har ila yau, ya ce a kudancin kasar kuwa, dakarun na aikin dakile mayakan kungiyar IPOB dake neman kafa kasar Biafra. (Fa’iza Mustapha)